"In da ni ne shugaban kasa, da tuni Obasanjo ya dade da kwana gidan yari" - Wani jigon APC

"In da ni ne shugaban kasa, da tuni Obasanjo ya dade da kwana gidan yari" - Wani jigon APC

Jigo a jam'iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan jihar Edo dake a kudu-maso-kudancin Najeriya Kwamarade Adams Oshiomhole a jiya ya bayyana cewa da shi ne shugaba Buhari da tuni tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo yana gidan yari.

Tsohon gwamnan dai wanda yanzu haka yake neman takarar zama shugaban jam'iyyar APC na kasa yayi wannan kalaman ne a lokacin da ya samu tubarrakin daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar Cif Bola Tinubu da kuma gwamnonin jam'iyyar game da kudurin sa.

"In da ni ne shugaban kasa, da tuni Obasanjo ya dade da kwana gidan yari" - Wani jigon APC

"In da ni ne shugaban kasa, da tuni Obasanjo ya dade da kwana gidan yari" - Wani jigon APC
Source: Depositphotos

KU KARANTA: PDP tayi karin haske game da dan takarar ta da zai kalubalanci Buhari

Legit.ng ta samu cewa a kwanan baya nan ne dai Cif Obasanjo din ya fitar da wata takardar manema labarai da a cikin ta ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da kokarin daure shi da nufin hana shi adawar da yake yi da ita.

A wani labarin kuma, Alkaliyar wata kotun tarayya dake zaman ta a garin Kano mai suna Mai shari'a Zainab Bage Abubakar ta haramtawa tsohon gwamnan jihar Kano, Alhaji Ibrahim Shekarau zuwa kasar Saudiyya don yi Umarah ta hanyar kin bashi fasfo din sa.

Tun farko dai, tsohon gwamnan na jihar Kano ya roki kotun ce da ta dubi girman Allah ta bashi fasfo din sa tun a ranar 28 ga watan Mayun da ya gabata domun ya samu damar zuwa yayi ibada a kasa mai tsarkin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel