Kudin makamai: Wata kotun tarayya ta haramtawa Shekarau zuwa Umrah

Kudin makamai: Wata kotun tarayya ta haramtawa Shekarau zuwa Umrah

Alkaliyar wata kotun tarayya dake zaman ta a garin Kano mai suna Mai shari'a Zainab Bage Abubakar ta haramtawa tsohon gwamnan jihar Kano, Alhaji Ibrahim Shekarau zuwa kasar Saudiyya don yi Umarah ta hanyar kin bashi fasfo din sa.

Tun farko dai, tsohon gwamnan na jihar Kano ya roki kotun ce da ta dubi girman Allah ta bashi fasfo din sa tun a ranar 28 ga watan Mayun da ya gabata domun ya samu damar zuwa yayi ibada a kasa mai tsarkin.

Kudin makamai: Wata kotun tarayya ta haramtawa Shekarau zuwa Umrah

Kudin makamai: Wata kotun tarayya ta haramtawa Shekarau zuwa Umrah
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun farwa wani babban soja a Arewa

Legit.ng ta samu cewa sai dai lauyan hukumar EFCC din dake karar sa gaban kotun bisa zargin sa da cin kudaden makamai a lokacin tsohuwar gwamnatin Jonathan ya ki yadda da bukatar hakan.

A wani labarin kuma, Jami'an tsaron rundunar 'yan sanda a jihar Katsina ta sanar da cewa ta shirya tsaf domin baza mutanen ta akalla dubu 3 da 500 a dukkan lungu da sakon jihar domin tabbatar da bayar da tsaro ga al'umma a yayin bukukuwan Sallah karama da ke tafe.

Wannan dai kamar yadda muka samu, na a matsayin kari ne ga wasu jami'an tsaron farin kaya watau Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) 500 da sojoji da ma wasu jami'an tsaron na daban da za'a kara bazawa a jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel