Kotu ta saka ranar yankewa Sule Lamido hukunci bayan ya gaza amsa tambayar lauyan EFCC

Kotu ta saka ranar yankewa Sule Lamido hukunci bayan ya gaza amsa tambayar lauyan EFCC

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya kasa bayar da amsar tambayar da lauyan hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ya yi masa a kan zargin sa da badakalar makudan kudade a gaban mai shari'a, Jastis Babatunde Quadri.

Don haka mai shari'a Quadri ya dage Sauraren karar zuwa ranar 27 ga watan Yuli, 2018, domin yankewa Sule Lamido hukunci a kan zargin sa da ake yi na dadakala da dukiyar al'ummar jihar jigawa.

Ana tuhumar tsohon gwamna sule Lamido tare da ‘ya’yan sa guda biyu, Aminu da Mustapha, da kuma wasu mutane biyu da cin amana da kuma wawure kudin jihar jigawa.

Kotu ta saka ranar yankewa Sule Lamido hukunci bayan ya gaza amsa tambayar lauyan EFCC

Sule Lamido a kotu

An zabi sule Lamido gwamnan jigawa a shekarar 2007 a karo na farko, kafin daga bisani a sake zaben sa a shekarar 2011 a karo na biyu.

Tun yana kan mulki ake korafin yadda Lamido ya mayar da ‘ya’yan sa shafaffu da mai ta hanyar basu manyan kwangiloli da kuma basa dammar yin katsalandan a harkokin tafiyar da gwamnati. Zargin da Sule Lamido ya yi kunnen uwar shegu da shi.

DUBA WANNAN: Na shiga sana'ar garkuwa da mutane ne domin samun kudaden hidimar sallah - Wani matashi

Ko a lokacin da yake gwamna, jami’an kwastam sun taba kama daya daga cikin ‘ya’yan sa da dalolin Amurka yana kokarin ficewa dasu daga Najeriya.

Lamido na daga cikin ‘yan PDP da a yanzu haka ke fatan ganin sun samu tikitin jam’iyyar domin yin takarar shugaban kasa a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel