12 ga watan Yuni: Yar Abiola, Hafsat ta ba shugaba Buhari hakuri

12 ga watan Yuni: Yar Abiola, Hafsat ta ba shugaba Buhari hakuri

Yarinyar shugaban kasa da ya lashe zaben 12 ga watan Yuni, 1993, Moshood Abiola ta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari hakuri kan lamarin da ya faru a tsakanin zaben Yuni 1993 da kuma mutuwar mahaifinta.

A wajen taron karrama mahaifinta da wasu mutane biyu da akayi a ranar 12 ga watan Yuni, Hafsat Abiola-Costello tace ana ganin abubuwa basu iya yiwuwa har sai anga faruwansu.

Da take ba shugaba Buhari tare da iyalansa hakuri, Hafsat tace abun al’ajabi ne yadda Allah yayi amfani da shugaban kasar wajen dawo da martabar mahaifinta.

12 ga watan Yuni: Yar Abiola, Hafsat ta ba shugaba Buhari hakuri

12 ga watan Yuni: Yar Abiola, Hafsat ta ba shugaba Buhari hakuri

A cewarta tayi amfani da wannan damar ta ba shugaba Buhari hakuri a madadin mahaifinta domin ta san abunda zai iya yi da ace yana raye.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shehu Sani sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar ya yabama shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa karramawar da yayiwa wanda ya lashe zaben June 12 1993, MKO Abiola.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni 7, Tinubu da Akande sun tsayar da Oshiomhole

A wani rubutu da ya wallafa a shafin twitter a ranar Laraba, 13 ga watan Yuni, dan majalisan yace karramawar da shugaban kasar yayi da kuma nuna muhimmancin yanci da ya nuna abun yabawa ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin samun ingantattun labarai, bide mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel