Abubuwan da muka tattauna jiya a taron da mu kayi da Buhari - Okorocha

Abubuwan da muka tattauna jiya a taron da mu kayi da Buhari - Okorocha

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya fede biri har wutsiya game da abubuwan da gwamnonin jam'iyyar APC suka tattauna a taron da su kayi da shugaba Muhammadu Buhari a yammacin jiya Talata.

Gwamnonin dai sunyi wata gannawar sirri ne da shugaba Buhari a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Taron da aka fara misalin karfe 9.10 na dare ya dauki tsawon sa'a guda kuma bayan fitowarsa daga taron, Okorocha wanda shine ciyaman din kungiyar gwamnonin APC ya ce dama al'ada ce gwamnonin su ziyarci shugaban kasa don tattauna abubuwan dake faruwa a jam'iyyar.

Abubuwan da muka tattauna a taron mu da Buhari - Okorocha

Abubuwan da muka tattauna a taron mu da Buhari - Okorocha

KU KARANTA: Ina cikin mutanen da aka zaba domin yin takara da Abiola - Boss Mustapha

Ya ce Ciyaman din kwamitin shirye-shiryen gangamin taron APC na kasa, Gwamna Abubakar Badaru na Jihar Jigawa ya yiwa shugaban kasa bayani kan shiryen-shiryen da aka gudanar a yanzu.

Ya kuma ce sun tattauna a kan yadda za su fuskanci kallubalen siyasa da za su rika kunno kai muddin lokacin zabe ya karato. Gwamnan Jihar Imo ya ce a halin yanzu kawunnan gwamnonin APC a hade ya ke wuri guda kuma a shirye suke tsaf don tunkarar zaben 2019.

Kazalika, Okorocha ya ce gwamnonin sunyi wa shugaban kasa jinjina da murna a kan canja ranar demokradiyyar Najeriya zuwa ranar 12 ga watan Yuni don karrama marigayi Cif Moshood Kashimawo Abiola wanda ya lashe zaben 1993.

Da akayi masa tambaya a kan rikice-rikicen da ke jam'iyyar APC, Okorocha ya ce babu wani rikici a jam'iyyar ta APC illa kananan rashin jituwa da ba'a rasa ba kuma hakan na faruwa a kowacce jami'iyyar siyasa.

"Ko tsakanin yan uwa yan gida daya akan samu rashin jituwa. Duk jam'iyyar da ba'a samun rashin jituwa ba jam'iyya bace," inji shi.

Sai dai gwamnan na Jihar Imo bai yi tsokaci akan rikicin da ke faruwa a jihar sa ba duk da cewa wasu sun ce ana kokarin korar sa daga jam'iyyar ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel