Karramawan da akayiwa Abiola abun yabawa ne amma kada ku bari a sha ku – Shehu Sani ga yan Najeriya

Karramawan da akayiwa Abiola abun yabawa ne amma kada ku bari a sha ku – Shehu Sani ga yan Najeriya

Shehu Sani sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar ya yabama shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa karramawar da yayiwa wanda ya lashe zaben June 12 1993, MKO Abiola.

A wani rubutu da ya wallafa a shafin twitter a ranar Laraba, 13 ga watan Yuni, dan majalisan yace karramawar da shugaban kasar yayi da kuma nuna muhimmancin yanci da ya nuna abun yabawa ne.

Sai dai kuma ya bayyana cewa kada yan Najeriya su kuskura su bari a sha su ko ayi masu wayo da wannan karramawa da akayiwa MKO Abiola.

Karramawan da akayiwa Abiola abun yabawa ne amma kada ku bari a sha ku – Shehu Sani ga yan Najeriya

Karramawan da akayiwa Abiola abun yabawa ne amma kada ku bari a sha ku – Shehu Sani ga yan Najeriya

A halin da ake ciki, yarinyar shugaban kasa da ya lashe zaben 12 ga watan Yuni, 1993, Moshood Abiola ta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari hakuri kan lamarin day a faru a tsakanin zaben Yuni 1993 da kuma mutuwar mahaifinta.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni 7, Tinubu da Akande sun tsayar da Oshiomhole

A wajen taron karrama mahaifinta da wasu mutane biyu da akayi a ranar 12 ga watan Yuni, Hafsat Abiola-Costello tace ana ganin abubuwa basu iya yiwuwa har sai anga faruwansu.

Da take ba shugaba Buhari tare da iyalansa hakuri, Hafsat tace abun al’ajabi ne yadda Allah yayi amfani da shugaban kasar wajen dawo da martabar mahaifinta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin samun ingantattun labarai, bide mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel