An fara aikin gina sabuwar matatar mai da zata ci dala biliyan 12

An fara aikin gina sabuwar matatar mai da zata ci dala biliyan 12

- Matatun mai sun yi kadan a kasar nan

- An sha alkawurran gina refinery a kasar nan

- Har yanzu Najeriya ta dogara da shigo da mai

An fara aikin gina sabuwar matatar mai da zata ci dala biliyan 12

An fara aikin gina sabuwar matatar mai da zata ci dala biliyan 12

An fara Ginin matatar man fetur na Azikel mai kimanin dala biliyan 12 a Obunagh Gbarain, a jihar Bayelsa wanda ya tada burikan kasuwar man fetur na gida.

A binciken da Vanguard tayi, ya nuna cewa an kusa gama Ginin matatar wanda ya kunshi tituna, katanga da sauransu.

A wata tataunawa da Vanguard tayi da mataimakin watsa labarai na shugaban kungiyar Azikel, Mista Austin Ebipade, ya bayyana cewa an gama aikin kusan kashi 75 cikin dari, ya kara da cewa har yanzu dai ba a sa ranar fara aiki ba.

Yace "watanni kadan da suka wuce, ba a gina gurin ma'aikatan ba da sauran gine gine duk fara su akayi, amma a yanzu maganar da muke yi, an kai kashi 85 na gine ginen, karashe kawai ya rage".

DUBA WANNAN: Babu Buhari a masu yi min juyin mulki

"A yanayin da aikin ke tafiya, zamu iya gamawa zuwa watan Disamba, 2018, muna fatan zamu fara aiyuka. Bama fata, amma in dai bamu fara nan da Disamba 2018 ba, zamu fara a farkon shekarar 2019."

Idan an kammala, matatar zata samar da karin ganga 12,000 a rana.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel