Cin hanci da rashawa ne babban hadari ga cigaban Afrika – Shugaba Buhari

Cin hanci da rashawa ne babban hadari ga cigaban Afrika – Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Cin hanci da rashawa a matsayin babban hadari ga cigaban Afrika.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne da ya karbi bakoncin mambobin diflomasiyya domin sha ruwa a fadar shugaban kasa a ranar Talata, 12 ga watan Yuni.

A cewarsa, cin hanci da rashawa da gurgunta cigaba da kuma karya damokradiyya da kuma doka.

Yace: “Kamar yadda na fada a jawabi na, idan bamu kashe cin hanci da rashawa ba toh shi zai kashe mu. hanci da rashawa da gurgunta cigaba da kuma karya damokradiyya da kuma doka.”

“Dole mu yaki cin hanci da rashawa domin mu kawo cigaba, arziki da kuma jin dadi ga mutanenmu.”

Cin hanci da rashawa ne babban hadari ga cigaban Afrika – Shugaba Buhari

Cin hanci da rashawa ne babban hadari ga cigaban Afrika – Shugaba Buhari

Akan harkar tsaro kuma, shugaban kasar ya ba da tabbacin cewa gwanatinsa na duk wani kokari day a dace domin kawo karshen ta’addanci.

Yace kasar Najeriya zata cigaba da hada kai da makwabtanta domin kawo karshen ayyukan ta’addanci.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda sojoji ke shan gwagwarmaya domin kare al’umman kasarsu yayinda su kuma suke kwace suna walawa

Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ta dauki duk wani mataki da ya kamata domin inganta tattalin arziki.

Sannan ya yi godiya akan ziyarar bude baki da suka kai masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin samun ingantattun labarai, bide mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel