Daga karshe dai yau Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2018

Daga karshe dai yau Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2018

- A karshe dai yau za'a rattaba hannu kan kasafin kudin bana bayan shafe watanni da yinsa

- Tun a watan Nuwamba ne shugaba Buharin ya mikawa majalisar dokoki kundin kasafin kudin 2018

- In dai aka sanya hannu yau kamar yadda aka tsara, to ya zama dai-dai ranar da aka sanya na shekarar da ta gabata 12, Yuni 2018

An dai rawaito cewa in banda shirye-shiryen da ake gudanarwa na girmama Marigayi tsohon dan takarar shugaban kasa Moshood Abiola da Babagana Kingibe tare da Chief Gani Fawehinmi the tun jiya Talata ma zai sanya hannu a kasafin don kawo karshen tsaikon da aka shafe watanni ana fuskanta, wata majiya ta shaiwa jaridar THISDAY.

Bayan canje-canje cikin kudin kasafin kudin 2018 Shugaba Muhammadu Buhari zai rattaba hannun kansa a yau

Bayan canje-canje cikin kudin kasafin kudin 2018 Shugaba Muhammadu Buhari zai rattaba hannun kansa a yau

Idan za’a iya tunawa shugaban kasa Muhammadu Buhari dai ya mikawa majalisa kundin kasafin kudin ne a watan Nuwamba, amma majalisar ba ta kai ga kammala nata bincike kwakwaf din ba har si bayan watanni shida.

Sannan kuma suka sake shafe karin wasu kwanaki 10 kafin su iya mika shi ga fadar shugaban kasa.

Majiyarmu ta shaida cewa tsaikon shugaba Muhammadu Buhari ya samu nan a rattaba hannu kan kasafin kudin ya biyon bayan nazartarsa da yake yi kafin sanya hannun.

Amma bayan duba wadancan canje-canje yau ake sanya rai tabbas zai rattabawa kasafin hannu domin zama doka a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

KU KARANTA: ‘Yan Najeriya na shirin darawa: Manyan Jiragen ruwa 6 sun iso Najeriya makare da kayan abinci da Fetir da Taki

Idan dai har shugaba Buharin ya sanyawa kasafin hannu yau (12 Yuni, 2018), hakan zai kara maimaita yadda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya rattaba hannu kan kasafin shekarar da ta gabata ranar 12 Yuni, 2017, a lokacin yana mukaddashin shugaban kasa, bayan da majalisar dokoki ta zartar da shi a ranar 5 ga watan Mayu 2017.

Bayan canje-canje cikin kudin kasafin kudin 2018 Shugaba Muhammadu Buhari zai rattaba hannun kansa a yau

Bayan canje-canje cikin kudin kasafin kudin 2018 Shugaba Muhammadu Buhari zai rattaba hannun kansa a yau

Shugban kasa Muhammadu Buhari dai ya mikawa majalisar dokokin bukatarsa na amincewa da N8.6t a matsayin kasafin kudin 2018 amma sai majalisar tayi karin N508b ya koma N9.1t, a bisa dalilin karuwar bukatar da wasu sassa suke da shi da suka hada da tsaro, lafiya wutar lantarki aiyuka da kuma gidaje.

‘Yan Najeriya da dama sun bayyana fargabarsu ko rashin zartar da daftarin kasafin akan lokaci da majalisar ta gaza yi zai shafi lafiyar tattalin arzikin da bai gama farfadowa daga mashassharar da yayi ta matsin tattalin arziki ba.

Daga cikin wadanda aka fi jin amonsu kan waccan farga har da wani masanin harkar kudi dake aiki a kamfanin Financial Derivatives Company Limited wato Mr. Bismarck Rewane.

Inda yayi kira da babbar murya kan lallai-lallai shugaba Buharin ya tabbata ya rattaba hannu kan kasafin nan take domin cigaba da jan kafa ka iya kawo tasgaro ga tattalin arzikin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel