Tsautsayi baya wuce ranarsa: Wani katafaren gini ya ruguzo akan wasu Leburori 4

Tsautsayi baya wuce ranarsa: Wani katafaren gini ya ruguzo akan wasu Leburori 4

Hukumar Yansandan jihar Enugu ta tabbatar da mutuwani mutum tare da jikkatar wasu mutane a sakamakon rugujewar wani katafaren gidan sama hawa daya a daidai lokacin da ake tsaka da gina shi, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Ebere Amaraizu ta tabbatar da kisan, inda tace lamarin ya faru ne a ranar Talata a unguwar Ibeku Opi cikin karamar hukumar Nsukka na jihar Enugu.

KU KARANTA: Ana kashe kashe a Zamfara, Gwamna Yari yana tura mutane 5 kallon gasar cin kofin Duniya a Rasha

Ginin ya ruguzo ne a daidai lokacin da leburorin suke kokarin fara yi ma bangon ginin fulasta ne, inda ya rutsa da leburori guda hudu, wanda aka samu ceto su da kyar da sudin goshi, amma wani guda da ta rutsa da shi a waje daban ya rasu.

Tsautsayi baya wuce ranarsa: Wani katafaren gini ya ruguzo akan wasu Leburori 4

Wani Gida

Kaakakin ta ce tare da jami’an Yansanda aka ceto mutanen, inda ba tare da wata wata ba suka garzaya dasu zuwa babban asibitin Osondu, yayin da shi kuma wanda ya rasu mai suna Junior Afachaw aka mika gawarsa zuwa dakin ajiye gawa na Asibitin Shanaham.

Daga karshe rundunar Yansandan tace sun kaddamar da bincike kan lamarin, don gano musabbabin hatsarin da ya auku.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel