Kwakwaf: Kwamitin shugaban kasa ta bankado naira biliyan 2 da aka karkatar

Kwakwaf: Kwamitin shugaban kasa ta bankado naira biliyan 2 da aka karkatar

Wani Kwamiti na musamman da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa ta bankado wasu makudan kudade da yawansu ya kai dala miliyan 7, kwatankwacin naira biliyan 2.1 kenan da aka karkatar dasu, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamitin ta gano kudaden ne a wani asusun bankin Heritage, inda aka boye su da nufin daukesu idan kura ta lafa, kamar yadda shugaban kwamitin, Okoi Obono-Obla ya bayyana yayin mika rahotonsa ga Buhari.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya umarci Musulmai su nemi watan Shawwala daga Alhamis

Oblah ya shaida ma Buhari cewa sun gano naira miliyan 533 da kuma wani katafaren fili da darajarsa ta kai naira biliyan 1.5, dukkaninsu mallakin tsofaffin shuwagabannin hukumar bankin NEXIM, haka zalika kwamitin ta kwato naira miliyan 24 da tsofaffin hukumar wata hukumar Gwamnati suka sace.

Bugu da kari, Oblah yace sun kwatar ma hukumar kulawa da tashoshin jiragen ruwa, NPA, kasonta daga Otal din Agura, wanda wasu manyan mutane suka kwace mata sama da shekaru 20 da suka gabata.

Oblah bai tsaya nan har sai da ya tabbatar ma shugaban kasa Muhammadu Buhari cewar kwamitinsa ra kwato manyan motocin alfarma guda 19 daga hannun tsofaffun kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa, bayan sun arce dasu.

Daga karshe ya karkare da cewa a yanzu haka kwamitinnasa ta hada hannu da babban sakataren kasar Birtaniya don hana mutanen da ake tuhuma da satar kudaden al’umma daga neman mafaka a kasar ta Birtaniya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel