Kwankwaso na shirin tattara komatsansa da shi da wasu jigogin APC zuwa wata sabuwar Jam’iyya

Kwankwaso na shirin tattara komatsansa da shi da wasu jigogin APC zuwa wata sabuwar Jam’iyya

- Sanata Abulaziz Nyako ya bayyanawa cewa suna nan suna tattaunawa da wasu Sanataci ciki har da Rabiu Musu Kwankwanso domin shirye-shiryen kafa wata sabuwar Jam'iyya

- Indai wannan yunkuri ya tabbata jam'iyyar APC lallai tayi babbar asarar jigogin da suka bayar da gudunmawar samun nasararta a zaben 2015

Nyako wanda shi ne Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya ya ce yana nan yana yin duk wata mai yiyuwa domin ganin ya samu magoya baya domin ficewa daga Jam'iyya mai mulki (APC) kamar yadda ya bayyana cewa ana nuna musu san kai da kuma nuna bangarenci, wanda hakan shi ne dalilin da zai sa su kafa wata sabuwar Jam'iyyar kamar yadda jaridar Premium times ta hada rahoton.

Kwankwaso na shirin tattara komatsansa da shi da wasu jigogin APC zuwa wata sabuwar Jam’iyya

Kwankwaso na shirin tattara komatsansa da shi da wasu jigogin APC zuwa wata sabuwar Jam’iyya

Ya ce "Wannan wani yunkuri ne kuma babu gudu balle ja da baya, yanzu haka ina shirya zama da manyan yam siyasa domin ganin yadda tafiyara tamu zata kasance. Na tattauna da Farfesa Jerry Gana na Jam'iyyar SDP, sai kuma Attahiru Bafarawa wanda shi kuma yake son ganin mun dawo Jam'iyyar PDP".

KU KARANTA: ‘Yan Najeriya na shirin darawa: Manyan Jiragen ruwa 6 sun iso Najeriya makare da kayan abinci da Fetir da Taki

"Ranar Alhamis din data gabata ma na ziyarci tsohon shugaban kasa Obasanjo a garin Abeokuta domin tattaunawa akan jam'iyyar ADC inda ya hada ni da hafsan soji Col. Oyinyola inda muka tattauna kuma ya tabbatar min da cewa zasu bamu hadin kai musamman wajen ganin mun cimma tsarinmu. Shi ma tsohon gwamnan Kano Kwankwanso na samu damar ganawa da shi dan ganin mun fito da sabuwar Jam'iyya".

"Tun wajen wata daya kenan aka bani kundin tsarin wannan sabuwar Jam'iyya tamu wanda nan ba da dadewa ba muke sa ran hukumar shirya zabe ta kasa INEC zata sahale mana wajen kafa wannan Jam'iyya".

Sannan ya kare bayaninsa da cewa yana matukar murna da farin ciki domin zasu fice daga Jam'iyyar APC tun lokaci bai kure musu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel