An yi gemu da gemu tsakanin Gwamnonion APC da shugaba Buhari a Villa (Hotuna)

An yi gemu da gemu tsakanin Gwamnonion APC da shugaba Buhari a Villa (Hotuna)

A daren Talata, 12 ga watan Yuni ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin tawagar gwamnonin jam’iyyar APC da suka kai masa ziyara a karkashin jagorancin shugabansu, Owelle Rochas Okorocha, gwamnan jihar Imo.

Da isarsu Villa, sai aka yi musu iso zuwa Ofishin uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, inda Buhari ya iskesu anan da misalin karfe 9 dai dai, ba tare da wata wata ba aka shiga goga gemu da gemu.

KU KARANTA: Ana kashe kashe a Zamfara, Gwamna Yari yana tura mutane 5 kallon gasar cin kofin Duniya a Rasha

An yi gemu da gemu tsakanin Gwamnonion APC da shugaba Buhari a Villa (Hotuna)

Taron

Wannan taro ya zo ne akan gaba, yayin da jam’iyyar ta shirya tsaf don zaben sabbin shuwagabanninta, musamman kujerar shugaban jam’iyya, wanda Buhari ya nuna ya fi kaunar tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole a matsayin angon jam’iyar.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na jihar Kogi, Yahaya Bello, na jihar Katsina, Aminu Bello Masari, Kwara Abdul Fatah Ahmed, Adamawa Bindow Jibrilla.

An yi gemu da gemu tsakanin Gwamnonion APC da shugaba Buhari a Villa (Hotuna)

Taron

Sauran sun hada da Gwamnan jihar Edo, Obaseki, Kebbi, Atiku Bagudu, Kano Abdullahi Ganduje, Jigawa, Badaru Talamiz, Benuwe, Samuel Ortom da kuma na Ogun, Ibikunle Amosun.

An yi gemu da gemu tsakanin Gwamnonion APC da shugaba Buhari a Villa (Hotuna)

Taron

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel