Goron Sallah: Gwamna Ganduje zai biya Albashin Watan Yuni ga Ma'aikatan Jihar Kano

Goron Sallah: Gwamna Ganduje zai biya Albashin Watan Yuni ga Ma'aikatan Jihar Kano

Gidan Talabijin na Najeriya watau NTA ya ruwaito cewa, Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da lamunin biyar Albashin watan Yuni ga ma'aikatan Jihar sa wanda za a fara gudanarwa a ranar yau ta Laraba.

Mun samu wannan rahoto ne a ranar Talatar da ta gabata da ya bayyana cewa, gwamnan ya bayar da amincewar sa na biyan Albashin da wuri domin bai wa ma'aikatan jihar sa dama ta gudanar da Hidindimu da Shagulgula na bikin Sallah cikin Farin ciki da Annashuwa tare da Iyalan su.

Goron Sallah: Gwamna Ganduje zai biya Albashin Watan Yuni ga Ma'aikatan Jihar Kano

Goron Sallah: Gwamna Ganduje zai biya Albashin Watan Yuni ga Ma'aikatan Jihar Kano

A sanadiyar haka ne gwamnan ya umarci Bankunan jihar akan tabbatar da ma'aikatan sun samu Albashin su cikin sauƙi.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya bai wa 'Yan Najeriya Hakuri dangane da soke Zaben 12 ga Yunin 1993

Legit.ng ta fahimci cewa, Gwamnan ya yi wannan tagomashi domin inganta jin dadin M'aikatan sa tare da gwangwaje su yayin shagulgulan Sallah.

Gwamnan ya kuma nemi Ma'aikatan Jihar akan kamanta wannan kyakkyawar gudunmuwa ta jajircewa da tsayuwar daka yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyan su wajen gudanar da ayyukan su domin tabbatar da ci gaban jihar.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Talatar da ta gabata takwaran Ganduje na jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu, ya yi wannan makamanciyar tagomashi ga ma'aikatan jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel