Nigerian news All categories All tags
Sarkin Musulmi ya umarci Musulmai su nemi watan Shawwala daga Alhamis

Sarkin Musulmi ya umarci Musulmai su nemi watan Shawwala daga Alhamis

Hukumar koli ta shariar Musulunci, NSCIA, dake karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ta umarci al’umma Musulmai dasu fita neman watan Shawwal, watan Sallah a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuni, daidai 29 ga watan Ramadan.

Daily Trust ta ruwaito mataimakin babban sakataren mulki na hukumar, Farfesa Salisu Shehu ne ya bada sanarwar a ranar Talata, 12 ga watan Yuni, inda yace idan har mutanen kirki daga cikin Musulmai suka hangi watan, Sarkin Musulmi zai sanar da Juma’a a matsayin 1 ga watan Shawwal.

KU KARANTA: Ana kashe kashe a Zamfara, Gwamna Yari yana tura mutane 5 kallon gasar cin kofin Duniya a Rasha

“Idan kuma ba’a hangi watan ba, ya zama kenan sallah zai kama ranar Asabar, 16 ga watan Yuni, 1 ga watan Shawwal kenan, don haka ake kira ga Musulmai dasu fita neman watan.” Inji Farfesan.

Sarkin Musulmi ya umarci Musulmai su nemi watan Shawwala daga Alhamis

Watan

Mai alfarma Sultan ya taya Musulmai ganin karshen Azumin Ramadan, haka nan yayi adduar Allah ya amshi ayyukan ibadun da Musulmai suka yi a wannan watan, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Daga karshe sanarwar ta karkare da kira ga Musulmai da su fitar da zakkar fidda kai, wato zakkar kunu da nufin tallafa ma gajiyayyun cikinsu, sa’annan ta yi gargadi da kada a dinga karkatar da kayan abincin zuwa inda bai kamata ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel