Mutane 40 sun shiga Hannu da Laifin yada Jita-Jita a Dandalin Sada Zumunta

Mutane 40 sun shiga Hannu da Laifin yada Jita-Jita a Dandalin Sada Zumunta

Mun samu rahoton cewa hukumar 'yan sanda ta kasar India ta cafke mutane 40 a Arewa maso Gabshin jihar Assam da laifin yada jita-jita akan masu satar yara da kuma kalamai na nuna kiyayya shafukan su na dandalan sada zumunta.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, wani babban jami'in dan sanda na kasar, G.V. Siva Prasad shine ya bayar da wannan rahoto yayin ganawa da manema labarai a ranar Talatar da ta gabata.

Babban jami'in ya bayar da shaidar cewa, hukumar ta cafke wannan mutane ne bayan kisan gillan wasu matasa biyu a jihar ta Assam a daren ranar Juma'ar da ta gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan mutane arba'in da suka shiga hannu sun banbanta da mutane 25 da hukumar ta cafke da ake zargin hannun su cikin kisan matasan biyu a babbar hanyar Karbi Anglong dake jihar Assam.

Mutane 40 sun shiga Hannu da Laifin yada Jita-Jita a Dandalin Sada Zumunta

Mutane 40 sun shiga Hannu da Laifin yada Jita-Jita a Dandalin Sada Zumunta

Rahotanni sun bayyana cewa, daruruwan 'yan banga sun yi tarayya wajen lakadawa matasan biyu duka har lahira yayin da suke ziyarar buda idanu a wani kauye dake babban birnin Assam na Guwahati.

KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya dake Nahiyyar Turai sun Jinjinawa Shugaba Buhari dangane da Karamcin Ranar 12 ga Watan Yuni

Kafofin watsa labarai na kasar sun wallafa sunayen wannan matasa kamar haka; Nilotal Das mai shekaru 29 da kuma Abhijeet Nath mai shekaru 30 a duniya da 'yan bangar suke zargin su da satar yara.

Ministan harkokin cikin gida na kasar, Sarbananda Sonowal, ya yi gargadi gami da kashedi ga al'ummar Kasar masu yada jita-jita a shafukan su na dandalan sada zumunta tare da jan kunnen su dangane da matsanancin hukunci da ka iya biyo bayan hakan.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Juma'ar makon da ya gabata ne wani matashi dan kasar Faransa ya kashe kansa a Masallacin mai Alfarma na Birnin Makkah.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel