Da duminsa: Shugaba Buhari ya yi wasu sabbin nadi 3, ya kuma sabunta wa'adin wasu shugabanin hukumomi 6

Da duminsa: Shugaba Buhari ya yi wasu sabbin nadi 3, ya kuma sabunta wa'adin wasu shugabanin hukumomi 6

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sabunta wa'adin wasu shugabanin hukumomin gwamnatin tarayya shida.

Shugaban kasan kuma har ila yau ya nada sabbin shugabanin wasu hukumomin gwamnatin tarayya tare da nada wani sabon mashawarci na musamman.

Ga sunayen shugabanin hukumomin da aka sabunta wa'adinsu tare da hukumominsu

1. Dr. Boboye Olayemi Oyeyemi (MFR) - Hukumar kiyaye haddura na kasa FRSC

2. Dr. Ja'afaru Alunua Momoh - Babban Direkan Asibitin Tarayya na Abuja

3. Dr. Nwadinigwe Cejetan Uwatoronye - Babban Direkta, Asibitin Kashi na Tarayya, Jihar Enugu

4. Farfesa Eli Jidere Bala - Direkta Janar, Cibiyar Makamashi ta kasa

5. Dr. Mohammed Jibrin - Direkta Janar, National Board of Technology Incubation

6. Farfesa Mihammed Haruna - Mataimaki na musamman, Cibiyar tsare-tsaren Kimiyya da fasaha na kasa

Sabbin nadin kuma da a kayi sune:

1. Dr Aliyu Adamu - Shugaban Kwallejin Ilimin (Fasaha) ta jihar Gombe

2. Dr. Yaya Baba Adamu - Medical Direka, Cibiyar Lafiya na Tarayya, Keffi, Jihar Nasarawa

3. Shugaban kasan kuma ya nada sabon mashawarci na musamman a fannin harkokin kasashen waje, Yahaya Lawal, zai fara aikinsa a ranar 1 ga watan Afrilun 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel