Ke duniya: Ki tausaya min, ke ma fa Kirista ce – Karanta yadda Dariye ya dinga rokon alkaliya

Ke duniya: Ki tausaya min, ke ma fa Kirista ce – Karanta yadda Dariye ya dinga rokon alkaliya

A yau ne wata babbar kotun gwamnatin tarayya, karkashin mai shari’a, Adebukola Banjoko, dake zaman ta a Abuja ta tisa keyar tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, zuwa gidan yari na tsawon shekaru 14 ba tare da zabin biyan tara ba.

Saidai a wani yanayi mai kama da na was an kwaikwayo, Dariye, ya kaskantar da kai tare da yin rowan magiya ga alkaliyar kotun domin tayi masa sassauci.

Ke ma fa kirista ce, ya kamata ki tausaya min, ki yi min rangwame don girman Allah,” Dariye ya roki mai shari’a Banjoko.

Tun ana tsaka da karanta bitar shari’ar, da aka fara tun shekarar 2007, Dariye ya nemi izinin kotun domin yin amfani da bandaki. Lamarin da ya bawa wasu dake cikin kotun dariya.

Ke duniya: Ki tausaya min, ke ma fa Kirista ce – Karanta yadda Dariye ya dinga rokon alkaliya

Dariye ke share hawaye bayan yanke masa hukunci

Ke duniya: Ki tausaya min, ke ma fa Kirista ce – Karanta yadda Dariye ya dinga rokon alkaliya

Dariye cikin kwalla

Ana tuhumar Dariye da laifin karkatar da biliyan N1.162 daga asusun jihar Filato lokacin zangon mulkin sa daga shekarar 1999 zuwa 2006.

An fara zaben Dariye a matsayin gwamnan jihar Filato a shekarar 1999 kafin daga bisani a sake zabar sa a karo na biyu a shekarar 2003, saidai an tsige shi a shekarar 2006 kafin daga bisani kotu tayi umarnin a mayar das hi ya karasa zangon mulkin sa a shekarar 2007.

DUBA WANNAN: Yadda Abacha ya yaudare mu, yanzu kowa kallon maciya amana yake mana - Kamfen darektan Abiola

Bayan kamala zangon mulkin san a biyu ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da shi gaban kotu a watan Mayun 2007 a kan wasu laifuka 21 da suka hada da wawure kudi tare da fitar da su kasashen ketare ta hanyar amfani da ofishin sa na gwamna.

Duk kokarin Dariye na ganin hukumar EFCC bata cigaba da tuhumar sa bay a ci tura bayan wata kotun tarayya ta soke hukuncin wata kotu da ta dakatar da sauraron karar na tsawon shekaru 7 tare da umarnin cigaba da tuhumar sa a shekarar 2015.

Ke duniya: Ki tausaya min, ke ma fa Kirista ce – Karanta yadda Dariye ya dinga rokon alkaliya

Yayin raka tsohon gwamna Dariye gidan yari bayan yanke masa hukunci

Ke duniya: Ki tausaya min, ke ma fa Kirista ce – Karanta yadda Dariye ya dinga rokon alkaliya

Dariye bayan an yanke masa hukunci

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel