Yan garin su Abiola na so a kara wa Buhari wa’adin mulki

Yan garin su Abiola na so a kara wa Buhari wa’adin mulki

Basaraken garin marigayi MKO Abiola, wanda ya lashe zabe a ranar 12 ga watan Yunin 1993, ya bukaci a kara wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin kwanaki 14 bayan kammala zangon sa na 2019.

Ya yi haka ne domin su na so a rantsar da shugaban da ya yi nasara a zaben 2019 a ranar 12 ga watan Yuni, 2019, tunda ita ce ranar da shugaba Buhari ya maida ranar Dimokradiyya.

Tun bayan da aka rantsar da Olusegun Obasanjo a matsayin shugaba a ranar 29 ga watan Mayun 1999, sai aka maida wannan rana a matsayin ranar dimokradiyya, kuma ita ce ranar da ake rantsar da sabbin shugabanni a matakin kasa da jihohi.

Yan garin su Abiola na so a kara wa Buhari wa’adin mulki

Yan garin su Abiola na so a kara wa Buhari wa’adin mulki

Sai dai kuma basaraken Gbagura, cikin jihar Ogun, garin da aka haifi Abiola, ya bayyana wa manema labarai cewa ai ya zama lallai a maida ranar mika mulki ta koma ranar 12 ga Yuni, domin ta hakan ne za a kara tabbatar da sahihanci da karbuwar zaben na 12 ga Yuni, 1993 da nufin raya fafutikar da MKO Abiola ya yi, wadda ita ce sanadin ajalin sa a tsare.

KU KARANTA KUMA: Kalli hotunan 'yan wasan Super Eagles a yayinda suka isa kasar Rasha

A halin da ake ciki, wani dan takarar gwamna a karkashin inuwar APC a zaben jihar Osun da zaa yi a ranar 22 ga watan Satumba, Alhaji Moshood Olalekan Adeoti ya shawarci tsohon shugaban kasa a mulkin soja, janar Ibrahim Babangida da ya ba yan Najeriya hakuri akan juyin mulkin 12 ga watan Yunin 1993.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin samun ingantattun labarai, bide mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel