Za mu fice daga jam'iyyar APC - Nyako

Za mu fice daga jam'iyyar APC - Nyako

Abdul-Azeez Nyaku, sanata mai wakiltan Adamawa ta tsakiya ya ce ya fara shirin fice wa daga jam'iyyar APC tare da magoya bayan mahaifinsa tsohon gwamnan jihar Adamawa saboda yadda aka mayar da su saniyar ware.

Mista Nyako ya bayar da wannan sanarwan ne lokacin da ya ke jawabi ga magoya bayansa a birnin Yola.

Mista Nyako ya ce an juya musu baya a zabubukan kananan hukumomi da taron jam'iyyar da akayi inda aka zabi mahukunta jam'iyyar. Ya ce har mahaifinsa, Murtala Nyako ya rasa gundumarsa dake karamar hukumar Mayo-Belwa.

Za mu fice daga jam'iyyar APC - Nyako

Za mu fice daga jam'iyyar APC - Nyako

KU KARANTA: Mohamed Salah ya yi barazanar barin Liverpool

Ya ce tattaunwar sulhu da akeyi tsakanin shugabanin jam'iyyar APC da mambobin sabuwar PDP (nPDP) da a yanzu suke cikin APC ba zai haifar da wani da mai ido ba saboda yaudarar su kawai za'ayi.

"A ranar Alhamis, na tafi zuwa Abeokuta inda na tattauna da tsohon shugaban kasa Obasanjo a kan ADC. Ya umurce ni in ga Kwanel Oyinlola wanda ya bamu tabbacin za'a karbe mu hannu biyu-biyu idan zamu dawo jam'iyyar. Na kuma yi magana da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso kafin ayi gangamin taron jam'iyyar."

Mista Nyako ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso ya fada masa akwai wata sabuwar jam'iyya ta za'a kafa.

"An bani kundin tsarin jam'iyyar a watan da ta wuce, sabuwar jam'iyya ne kuma ana sa ran hukumar INEC za ta amince da ita tare da wasu jam'iyoyin guda hudu," inji Mista Nyako.

Mista Nyako ya ce yana matukar murnar barin jam'iyyar APC kafin lokaci ya kure musu. Ya kuma yi fatan cewa wannan lokacin barin jam'iyyar APC da zasuyi zai zama abin alkhairi ba kamar yadda suka baro PDP zuwa APC ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel