Ana kashe kashe a Zamfara, Gwamna Yari yana tura mutane 5 kallon gasar cin kofin Duniya a Rasha

Ana kashe kashe a Zamfara, Gwamna Yari yana tura mutane 5 kallon gasar cin kofin Duniya a Rasha

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin gwamnan jihar, Abdul Aziz Yari ta dauki nauyin mutane biyar don zuwa kallon gasar cin kofin Duniya na bana da zai guda a kasar Rasha, a daidai lokacin da jihar ke fuskantar matsalar kashe kashen jama’a.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito kwamishinan al’amuran wasanni na jihar, Abdullahi Gurbin Bore ya tabbatar da tafiyar, inda yace shi ne zai jagoranci tawagar mutane biyar.

KU KARANTA: June 12: Ba zamu lamunci soke zabe a Najeriya ba, Dan ba kara – Buhari

Ana kashe kashe a Zamfara, Gwamna Yari yana tura mutane 5 kallon gasar cin kofin Duniya a Rasha
Tawagar yan kwallon Najeriya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mutanen da gwamnatin ta dauki nauyinsu zuwa Rasha sun hada da Kwamishinan wasanni, shugaban kwamitin wasannin motsa jiki na majalisar dokokin jihar, hadimi na musamman ga gwamnan jihar akan harkokin wasanni, babban daraktan hukumar wasanni na jihar da kuma shugaban kungiyar kwallo kafa reshen jihar Zamfara.

Duk dayake dai kwamishina Abdullahi bai bayyana adadin kudin da za’a kashe ba, amma ya bada tabbacin gwamna Abdul Aziz Yari ya amince da tafiyar.

A wani labarin kuma, Kwamishinan ya sanar da cigaba da biyan kudin alawus alawus da gwamnatin jihar ke biyan yan bautan kasa a baya, inda yace zasu dinga biya likitoci yan bautan kasa N50,000 jami’an kiwon lafiya dake bautan kasa a jihar zasu samu N20,000, sauran kuma naira dubu biyar biyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel