Bamu ci amanar Abiola ba, Abacha ne ya yaudare mu bakidaya - Kamfen darektan Abiola

Bamu ci amanar Abiola ba, Abacha ne ya yaudare mu bakidaya - Kamfen darektan Abiola

Darektan neman yakin zaben marigayi Moshood Bashorun Abiola, Jonathan zwingina, ya bayyana cewar duk ‘yan jam’iyyar SDP da suka yi aiki tare da Abacha, sun yi ne da izinin Abiola.

Zwingina na wadannan kalamai ne a yau, Talata, a wani shirin gidan Talabijin na Channels da ake nunawa kowacce safiya.

Ni ne sakataren kusan duk wani taro da tattaunawa da aka yi kafin da kuma bayan zaben ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993, kuma har yanzu ina iya tuna dukkan abinda ya faru hard a umarnin da Abiola ya bamu na yin aiki tare da gwamnatin soja ta Abacha bisa tsammanin cewar zai mika mulki ga Abiola bayan watanni 6 ko 12,” a cewar Zwingina.

Bamu ci amanar Abiola ba, Abacha ne ya yaudare mu bakidaya - Kamfen darektan Abiola

Abacha da Abiola

Zwingina ya kara da cewa, “wannan shine abinda ya faru. Ba wai mun gudu mun bar Abiola ba ne kamar yadda kafafen yada labarai ke rawaitowa ba.”

DUBA WANNAN: Abinda zan yi idan na rasa shugabancin jam'iyyar APC - Oshiomhole

Kazalika, yak are ragowar mutane irin su Kingibe, tsohon gwamnan jihar Legas, Lateef Jakande da lauya Olu onagoruwa (SAN) da suka yi aiki tare da gwamnatin soja ta Abacha tare da bayyana cewar har yanzu yana da kwafin takardun ganawar su da Abiola inda ya basu umarnin shiga gwamnatin soja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel