Manyan kwalekwale sun yi taho mu gama a cikin Tafki, mutane 10 sun ce ga garinku

Manyan kwalekwale sun yi taho mu gama a cikin Tafki, mutane 10 sun ce ga garinku

- Hatsarin jiragen ruwa ya faru a kasar Rasha

- Mutane 10 sun mutu, 5 sun jikkata, 1 ya bace

Akalla mutane goma ne suka rigamu gidan gaskiya a sakamakon wani mummunan hadari da ya rutsa dasu a cikin tafkin garin Volgograd dake kasar Rasha, kasar dake daukar nauyin gasar cin kofin Duniya na bana, inji rahoton jaridar Punch.

KU KARANTA: June 12: Mu Yarbawa za muyi ma Buhari ruwan kuri’u – Inji Bola Tinubu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Talata, 12 ga watan Yuni bayan da wani jirgi dake dauke da mutane 10 masu shawagi a cikin tafkin ta yi taho mu gama da wani karamin jirgin ruwa a tafkin Volga.

Manyan kwalekwale sun yi taho mu gama a cikin Tafki, mutane 10 sun ce ga garinku

Manyan kwalekwale

Sai dai daga cikin mutane sha shida dake cikin jirgin yawon, jami’a kwankwana sun yi nasarar ceto mutane biyar, inda a yanzu haka guda uku daga cikinsu na kwance a Asibiti, goma sun mutu, yayinda guda daya yayi batan Dabo, inji gwamnan yankin Andrei Bocharov.

A garin Volgograd za’a fara wasan cin kofin Duniy a tsakanin kasar Ingila, Tunisia, Najeriya, Iceland, Saudi Arabia, kasar Masar, Japan da kuma Poland.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel