Super Eagles sun lashe lambar yabo na tawagar da suka fi kwalliya a Rasha

Super Eagles sun lashe lambar yabo na tawagar da suka fi kwalliya a Rasha

Kungiyar yan Super Eagles sun amshi babban lambar yabo a matsayin tawagar da kayan tafiyarsu yafi kayatarwa.

Sun samu wannan karramawa ne daga kamfanin British Broadcasting Corporation (BBC), a kasar Rasha yan kwanaki kadan kafin fara wasar ci kofin duniya na 2018.

Hakan na kunshe ne a cikin mujallar kwalliya ta duniya GQ inda aka kiyasta kayan kwallon yan Najeriya a matsayin wanda yafi kyau a na yan kwallon 2018.

Super Eagles sun lashe lambar yabo na tawagar da suka fi kwalliya a Rasha

Super Eagles sun lashe lambar yabo na tawagar da suka fi kwalliya a Rasha

Yan wasan Najeriya sun isa kasar Rasha domin fafatawa a gasar cin kofin duniya ta 2018. Sun isa kasar ne cikin dare.

Za'a fara gwarawa ne a ranar 14 ga watan Yuni inda mai masaukin baki Rasha za ta bude filin da Saudiyya.

KU KARANTA KUMA: Kasar Ghana, da sauran kasashen Afrika zasu dunga siyan mai daga matatar Dangote

A ranar 16 ga wata ne Najeriya za ta soma karawa da kasar Croatia, wanda ya kunshi Iceland da kuma Argentina.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel