An rasa rayyuka da dama a wata mummunar hatsarin da ya afku a babban titin Legas zuwa Ibadan

An rasa rayyuka da dama a wata mummunar hatsarin da ya afku a babban titin Legas zuwa Ibadan

A kalla mutane takwas ne suka rasa rayyukansu a yau Talata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru tsakanin wata farar Toyota Hiace da wata Trela a babban titin Legas zuwa Ibadan.

Kakakin Hukumar kiyaye haddura ta jihar Ogun (TRACE), Mista Babatunde Akinbiyi ne ya tabbatar da afkuwar hatsarin ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a garin Abeokuta.

Akinbiyi ya ce yin gudu fiye da ka'ida da kuma overtaking ba bisa ka'ida ba da bus direban Bus din ya yi ne ya janyo hatsarin.

An rasa rayyuka da dama a wata mummunar hatsarin da ya afku a babban titin Legas zuwa Ibadan

An rasa rayyuka da dama a wata mummunar hatsarin da ya afku a babban titin Legas zuwa Ibadan

Ya ce fasinjoji bakwai da ke cikin bus din mai lamba BEN-313 YX sun mutu nan take yayin da fasinja guda kuma ya mutu bayan an kai shi asibiti.

KU KARANTA: Haihuwa ba tayi rana ba: An damke wani matashi da ya antayawa mahaifiyarsa ruwan zafi

"Hatsarin ya ritsa da mutane 10 ne baki daya - biyar maza, sannan sauran biyar din mata ne. Maza biyar da mata biyu sun mutu nan take, sannan mace daya ta mutu a asibiti.

"Abin da ya janyo hatsarin shine kubcewar motar da tayi wa direban bus na daukan fasinjoji da ya taso daga Legas a hanyarsa ta zuwa Benin inda ya buga wa Trela mai lamba MUS-730 XN da ke gabansa," inji shi.

Kakakin hukumar TRACE din ya kuma ce an ajiye gawawakin wanda suka rasu a asibitin koyarwa ta Jami'ar Olabisi Onabanjo da ke Sagamu, sauran wanda hatsarin ya ritsa da su suna karban magani a asbitin.

Kazalika, kwamandan hukumar kiyaye haddura na kasa FRSC na jihar, Mr Clement Oladele shima ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Oladele ya sake gargadi da direbobi da su kiyaye dokokin titi tare da kiyaye adadin gudu a kan tituna. Ya kuma yi kira ga fasinjoji su rika janyo hankalin direbobin motan da suka shiga saboda rai guda daya ce tak.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel