Shugaba Buhari ya bai wa 'Yan Najeriya Hakuri dangane da soke Zaben 12 ga Yunin 1993

Shugaba Buhari ya bai wa 'Yan Najeriya Hakuri dangane da soke Zaben 12 ga Yunin 1993

A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da hakuri a madadin gwamnatin tsohon shugaban Kasa, Ibrahim Badamasi Babangida, dangane da soke zaben da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993.

Tsohon Shugaban Kasa Badamasi Babangida ya soke zaben da ake da tabbacin nasarar Marigayi Cif MKO Abiola, inda shugaba Buhari ya nemi afuwar 'yan Najeriya dangane da wannan babban kuskure.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ta bayyana, shugaba Buhari ya bayar da wannan sanarwa ne yayin bikin karamcin da aka gudanar a fadar sa ta Villa inda ya tabbatar dawowar dimokuradiyya a gwamnatin kasar nan.

Shugaba Buhari ya bai wa 'Yan Najeriya Hakuri dangane da soke Zaben 12 ga Yunin

Shugaba Buhari ya bai wa 'Yan Najeriya Hakuri dangane da soke Zaben 12 ga Yunin

Shugaba Buhari ya karrama Marigayi Abiola da mafi kololuwar mukami a kasar nan na GCFR, tare da Fitaccen Lauya mai kare hakkin dan Adam Marigayi Cif Gani Fawehinmi, da kuma Ambasada Babagana Kingibe, abokin takarar Marigayi Abiola.

KARANTA KUMA: Yanzu-Yanzu: Uwargidan Fawehinmi da 'Dan sa sun isa Fadar Shugaban 'Kasa

Yake cewa, duk da kasancewar gwamnati ba ta ikon da dawo da shekarar 1993, ta na da ikon gyara kura-kuran da gwamnatin ta aikata a wannan lokuta.

A yayin haka shugaba Buhari ya nemi 'yan Najeriya su yi riko da wannan sabuwar ranar Dimokuradiyya da aminci da gaskiya.

Shugaban ya kara da cewa, Najeriya ba za ta sake lamuntar karkatar da adalci mai girman muni makamancin wannan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel