June 12: Mu Yarbawa za muyi ma Buhari ruwan kuri’u – Inji Bola Tinubu

June 12: Mu Yarbawa za muyi ma Buhari ruwan kuri’u – Inji Bola Tinubu

Jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci yin tazarce a kujerar shugaban kasa, don haka ya tabbatar da zai bada gudunmuwa sai inda karfinsa yak are, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Talata, 12 ga watan Yuni yayin bikin karrama tsohon hamshakin dan kasuwa, kuma fitaccen dan siyasa da ya yi takarar shugaban kasa a shekarar 1993 karkashin jam’iyyar SDP, Moshood Abiola da shugaba Buhari ya shirya a garin Abuja.

KU KARANTA: Kudin tsafi: Yadda wasu mutane 4 suka hallaka abokinsu suka guntule zuciyarsa

Dayake zayyana cigaban da gwamnatin Buhari ta samar, Tinubu yace a yanzu yan Najeriya na morar wutar lantarki ba kamar yadda suka yi ta fama da duhu ba a zamanin gwamnatocin baya.

June 12: Mu Yarbawa za muyi ma Buhari ruwan kuri’u – Inji Bola Tinubu

Tinubu da Buhari

Bugu da kari Tinubu ya jinjina ma gwamnatin Buhari duba da tsarin rage radadin talauci gay an Najeriya da ta bullo dasu, da suka hada da N-Power, ciyar da daliban Firamari Abinci, biyan 5,000 ga gajiyayyu da ire irensu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi jigon yana cewa karrama Abiola da Buhari yayi ya tabbatar da mafarkin al’ummar mutanen kudu maso yammacin kasar nan, don haka ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajen kwarara masa kuri’u a zabukan 2019.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel