'Yan Najeriya dake Nahiyyar Turai sun Jinjinawa Shugaba Buhari dangane da Karamcin Ranar 12 ga Watan Yuni

'Yan Najeriya dake Nahiyyar Turai sun Jinjinawa Shugaba Buhari dangane da Karamcin Ranar 12 ga Watan Yuni

Kamar yadda kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito mun samu rahoton cewa, 'yan Najeriya dake ƙetaren Nahiyyar Turai sun yabawa shugaban Kasa Muhammadu Buhari dangane da kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar Dimokuradiyya.

Hakazalika shugaban kasar ya samu yabo gami da jinjina dangane da karrama Marigayi Cif MKO Abiola a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 1993.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 6 ga watan Yunin da ta gabata ne shugaba Buhari ya bayar da umarnin kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar biki da tunawa da Dimokuradiyya sabanin ranar 29 ga watan Mayu da aka saba a kowace shekara.

Shugaba Buhari ya kuma zartar da ƙudurta ƙaddamar da wanda ya yi nasarar zaben shugaban kasa da aka soke sakamakon sa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993, Marigayi Cif Moshood Abiola wanda ya karrama da mafi kololuwar karamci a kasar nan.

Baya ga Abiola, shugaba Buhari ya kuma karrama wani fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam, Marigayi Cif Gani Fawehinmi da kuma abokin takarar Abiola, Alhaji Babagana Kingibe da karamci mafi kololuwar girma a mataki na biyu a kasar nan.

'Yan Najeriya dake Nahiyyar Turai sun Jinjinawa Shugaba Buhari dangane da Karamcin Ranar 12 ga Watan Yuni

'Yan Najeriya dake Nahiyyar Turai sun Jinjinawa Shugaba Buhari dangane da Karamcin Ranar 12 ga Watan Yuni

'Yan Najeriya dake Nahiyyar Turai sun Jinjinawa Shugaba Buhari dangane da Karamcin Ranar 12 ga Watan Yuni

'Yan Najeriya dake Nahiyyar Turai sun Jinjinawa Shugaba Buhari dangane da Karamcin Ranar 12 ga Watan Yuni

Dangane da wannan karamci, kungiyar 'yan Najeriya dake kasar Birtaniya da sanadin wani jagoranta, Mista Rowland Ikpi, ta yabawa shugaba Buhari da cewar wannan lamari ya tabbatar da gaskiya da darajar Dimokuradiyya a kasar nan.

KARANTA KUMA: Bagudu ya bayar da amincin Biyan Albashin watan Yuni ga Ma'aikatan Jihar Kebbi

Mista Ikpi yake cewa, shugaba Buhari ya taka rawar gani ta musamman da gwamnatocin baya suka gaza sakamakon mahangar su ta rashin ganin fa'idar wannan karamci da ya kamata tuni a an kaddamar a kasar nan.

Hakazalika wani dan Najeriya mai bincike a birnin Geneva na kasar Switzerland, Dakta Sachmicit Bancir, ya yabawa wannan ƙarfin hali na shugaba Buhari dangane da wannan ƙwazo na gyara kurakuran baya da suka afku a kasar nan.

Legit.ng ta fahimci cewa, an kafin shellar shugaba Buhari na kaddamar da sabuwar ranar Demokuradiyya, an saba gudanar da hutu a wannan rana cikin Jihohin Ekiti, Ondo, Ogun, Osun, Oyo da kuma Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel