Kasar Ghana, da sauran kasashen Afrika zasu dunga siyan mai daga matatar Dangote

Kasar Ghana, da sauran kasashen Afrika zasu dunga siyan mai daga matatar Dangote

Gabannin kammala matatar man Dangote, kasashen Afrika dake sufurin man fetur da masu rarraba mai a Ghana sun nuna daukin fara siyan mai daga dan Najeriya idan ya fara aiki.

Masu siyan man sunce yarjejeniya ya kammala domin safarar man fetur din dafa matata mafi girma a duniya, wanda ke Lekki, jihar Lagas sannan kuma mallakar mai kudin Afrika, Aliko Dangote.

An bayar da tsokaci kan dokin nasu ne a taron man fetur din kasar Ghana (Ghipcon 2018) wanda ake gudanarwa duk shekara, wanda aka yi a Accra, Ghana, a cewar sanarwa daga gidauniyar Dangote a ranar Litinin, 11 ga watan Yuni.

Wadanda suka halarci taron da kuma manyan masu rarraba maid a yan kasuwa daga kasashe daban-daban suna daukin sani yadda zasu dunga samun daga gangar mai 650,000 a ko wacce rana daga matatar, bisa ga sanarwan.

Kasar Ghana, da sauran kasashen Afrika zasu dunga siyan mai daga matatar Dangote

Kasar Ghana, da sauran kasashen Afrika zasu dunga siyan mai daga matatar Dangote

Gwamnatin kasar Ghana tace harka da Dangote zai fi kawo cigaba ga nahiyar Afrika maimakon dogaro da kasashen Turai.

KU KARANTA KUMA: Ina son Fati Washa kuma zan iya aurenta – Nuhu Abdullahi

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kasa Mahamud Bawumia, yace kasashen Afrika na nan suna jiran matatar Dangote.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel