Wata kungiya na zargin ana yi wa Saraki bita da kulli da zarge-zarge

Wata kungiya na zargin ana yi wa Saraki bita da kulli da zarge-zarge

- Saraki ya shiga tasku a hannun hukumomi tun 2015

- Ana gab da zabukan 2019 kuma watakil tadiya ce ake ma na ukun a kasar nan

- Zargin kin bin doka da oda, da ma wai daukar nauyin yan fashi ya dabaibaye shi a bana

Wata kungiya na zargin ana yi wa Saraki bita da kulli da zarge-zarge

Wata kungiya na zargin ana yi wa Saraki bita da kulli da zarge-zarge

Wata kungiya, mai suna Dynamic Patriotic Citizens (DPC) ta zargi wasu manya da biyan wasu don yin zanga zangar lumana ga yan majalisa tare da shugaban majalisar, Dr. Bukola Saraki.

Kungiyar tace an riga an gane shirin ne a satin da ya gabata sakamakon yunkurin tsige shi a cikin hanyoyi 12 na kawo gyara da aka bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi aiki a kai, bayan tataunawar hadaka da bangarorin biyu na majalisar suka yi inda sukayi barazanar tsige shugaban in ya kasa gyaran.

A wa magana ta sakataren shi na kasa, Shehu Mohammed, DPC ta zargi cewa bayan tallafin kudi da aka bada don zanga zangar ga yan majalisar, an tabbatar ma da masu zanga zangar zasu samu tsaro daga jami'an shugabancin kasar domin su samu damar bayyanawa da hargitsa aiyukan yan majalisar a sati mai gabatowa, sannan su nemi da a tsige Saraki da kuma manyan shuwagabanni 10 na majalisar.

DUBA WANNAN: An tona sirrin masu kokarin hana dimokuradiyya tun Abiola

Maganar tana cewa, "An sanar damu daga majiya mai karfi cewa wasu manya daga cikin jami'an shugabancin kasar nan zasu dau nauyin wasu kungiyoyi don yin zanga zangar lumana ga shugaban majalisar da kuma majalisar don asa su su janye yunkurin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari."

"Muna so mu wayar ma da yan Najeriya kai, su gane cewa banbancin mulkin soja da na farar hula shine majalisar zartarwa. "

"Zanga zangar lumana da aka shirya, bayan illar ta da rashin tsari, tana nufin durkushewar damokaradiyyar mu da kuma kokarin yan majalisar na ganin sun tabbatar da shugabanci na gari.

Abinda ke faruwa ya nuna cewa, majalisar mu ta 8 ba majalisar kawai bace. Saboda daya daga cikin kyawun damokaradiyya shine tankade da rairaya, yana kuma daga cikin aikin su, sa wa sauran zababbu ido don ganin suna tafiyar da mulkin su."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel