Yanzu Yanzu: Sojoji da yan banga sun dakile wani hari da Boko Haram suka kai Madagali an lalata gidaje 13

Yanzu Yanzu: Sojoji da yan banga sun dakile wani hari da Boko Haram suka kai Madagali an lalata gidaje 13

Wasu yan kungiyar yan ta’addan Boko Haram sun kai hari sannan sun lalata gidaje 13 a kauyen Kaya, karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa.

An tattaro cewa sojoji da yan banga sun dakile harin, inda suka kashe daya daga cikin yan ta’addan sannan suka raunata wani.

An rahoto cewa kungiyar sun lalata gidaje 13 sannan suka sace kayayyaki.

Yanzu Yanzu: Sojoji da yan banga sun dakile wani hari da Boko Haram suka kai Madagali an lalata gidaje 13

Yanzu Yanzu: Sojoji da yan banga sun dakile wani hari da Boko Haram suka kai Madagali an lalata gidaje 13

Gwamnatin jihar Adamawa, tayi jimami ga wadanda harin ya cika da su sannan ya yaba ma jarumtar sojoji da mutanen Madagali.

KU KARANTA KUMA: Jama’a sunyi cincirindo domin ganin gemun Manzon Allah a Turkiyya

Tayi wannan jimami ne tab akin kwamishinan bayanai na jihar Ahmed ya kuma bayyana cewa gwamnati na kokarin ganin taimako ya isa ga wadanda harin ya shafa cikin gaggawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel