Yanzu-Yanzu: Uwargidan Fawehinmi da 'Dan sa sun isa Fadar Shugaban 'Kasa

Yanzu-Yanzu: Uwargidan Fawehinmi da 'Dan sa sun isa Fadar Shugaban 'Kasa

Wani rahoto da sanadin shafin jaridar The Punch ya bayyana cewa, shirye-shirye ya kammala tsaf domin karrama Marigayi Cif Moshood Abiola, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993.

A yau ne ake gudanar da bikin tabbatar da nasarar Marigayi Abiola a Aso Villa inda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karrama shi da mafi kololuwar karamci ta mukamin GCFR (Grand Commander of the Federal Republic).

A yayin haka kuma, shugaba Buhari zai karrama fittacen Lauyan nan mai kare hakkin dan Adam, Marigayi Cif Gani Fawehinmi tare da abokin takarar marigayi Abiola, Babagana Kingibe da mukamin GCON (Grand Commander of the Order Niger).

Marigayi Cif Gani Fawehinmi

Marigayi Cif Gani Fawehinmi

Legit.ng ta fahimci cewa, an fara gudanar da wannan biki na karamci da misalin karfe 10.00 na safiyar a fadar ta shugaban Kasa dake babban Birnin Kasar nan na Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa Uwargidan Fawehinmi, Ganiat tare da Babban 'Dan sa, Muhammad, sun isa fadar ta shugaban Kasa domin halartar wannan biki na Karamci.

KARANTA KUMA: Wani Mutum ya Kashe Kansa a Masallacin Harami na Birnin Makkah

Muhammad Fawehinmi ya shaidawa manema labarai na fadar shugaban kasa cewa, ya na matukar farin ciki tare da alfahari dangane da yadda kokari gami da rawar da Mahaifin sa ya taka ba ta gushe ba a banza.

Hakazalika Ganiyat ta bayyana yadda Mijinta ya sha fama a hannun dakarun soji dangane da fafutikar sa wajen tabbatar da sakamakon gaskiya na zaben 12 ga watan Yunin 1993 da Marigayi Abiola ya lashe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel