Ba-kan-ta: 'Yan bindiga sun yi kwanton bauna sun kai wa babban janar din sojan Najeriya hari a Arewa

Ba-kan-ta: 'Yan bindiga sun yi kwanton bauna sun kai wa babban janar din sojan Najeriya hari a Arewa

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwa ye ba kawo yanzu mun samu labarin sun yi kwanton bauna inda suka kuma farma Manjo janar John Malu hari a kauyen sa na Tse Adoo dake a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue dake arewacin Najeriya.

Sai dai dai kamar yadda muka samu, cikin kankanin lokaci masu tsaron lafiyar sa suka mayar da martani ga 'yan bindigar suka kuma samu nasarar watsa su.

Ba-kan-ta: 'Yan bindiga sun yi kwanton bauna sun kai wa babban janar din sojan Najeriya hari a Arewa

Ba-kan-ta: 'Yan bindiga sun yi kwanton bauna sun kai wa babban janar din sojan Najeriya hari a Arewa

KU KARANTA: Atiku ya gargadi Buhari game da muzgunawa 'yan kasa

Legit.ng ta samu cewa kwamandan bataliyar sojojin ta 72 dake a jihar ta Benue Laftanal Kanal Suleiman Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin.

A wani labarin kuma, Injin helikwaftan da mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo yake ciki ne ya tsaya jim kadan bayan tashin shi a satin da ya gabata kamar dai yadda muka samu daga wani na kusa da mataimakin shugaban kasar Fasto Seyi Malomo.

Fasto Seyi Malomo ya bayyana hakan ne ga jama'a yayin da ya jagoranci addu'ar yi wa Allaha godiya da ya tseratar da mataimakin shugaban kasar a babbar cocin fadar shugaban kasa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel