12 ga watan Yuni: Atiku Abubakar ya yi wa Buhari da gwamnatin APC muhimmin gargadi

12 ga watan Yuni: Atiku Abubakar ya yi wa Buhari da gwamnatin APC muhimmin gargadi

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma mai neman tikitin takarar shugabancin kasar Najeriya a jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya gargadi shugaba Buhari da gwamnatin sa da su guji yi wa kundin tsarin mulkin kasar katsalandan domin moriyar su.

Alhaji Atiku Abubakar dai ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar daga ofishin kamfen din sa domin tunawa da soke zaben ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993.

12 ga watan Yuni: Atiku Abubakar ya yi wa Buhari da gwamnatin APC muhimmin gargadi

12 ga watan Yuni: Atiku Abubakar ya yi wa Buhari da gwamnatin APC muhimmin gargadi

KU KARANTA: Buhari, Osinbajo sun yi watsi da APC bayan zaben 2015

Legit.ng ta samu cewa a cikin sanarwar dai, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana shakkun sa game da yadda yace gwamnatin yanzu take yi wa yancin dan adam katsalandan domin kawai dalili na siyasa wanda yace hakan bai dace ba.

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta sake jaddada cewa ita fa har yanzu ba ta bai wa kowa tikitin takarar ta na shugaban kasar Najeriya a shekarar 2019 domin siyasa ce za'a buga sannan a fitar da dan takara.

Babban Sakataren gudanawar jam'iyyar a mataki na kasa Mista Austin Akobundu shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ya kuma rabwa manema labarai a garin Abuja.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel