Tsallake rijiya da baya: An gano matsalar da ta samu helikwaftan Osinbajo a satin da ya gabata

Tsallake rijiya da baya: An gano matsalar da ta samu helikwaftan Osinbajo a satin da ya gabata

Injin helikwaftan da mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo yake ciki ne ya tsaya jim kadan bayan tashin shi a satin da ya gabata kamar dai yadda muka samu daga wani na kusa da mataimakin shugaban kasar Fasto Seyi Malomo.

Fasto Seyi Malomo ya bayyana hakan ne ga jama'a yayin da ya jagoranci addu'ar yi wa Allaha godiya da ya tseratar da mataimakin shugaban kasar a babbar cocin fadar shugaban kasa.

Tsallake rijiya da baya: An gano matsalar da ta samu helikwaftan Osinbajo a satin da ya gabata

Tsallake rijiya da baya: An gano matsalar da ta samu helikwaftan Osinbajo a satin da ya gabata

KU KARANTA: Yar Najeriya ta samu 'yan 3 bayan shafe shekaru 13 tana neman haihuwa

Legit.ng dai ta tuna cewa a cikin satin da ya gabata ne jirgin mataimakin shugaban kasar yayi saukar gaggawa jim kadan bayan ya daga lokacin da ya halarcin bikin yaye manyan jami'an hukumar kwastam a unguwar Gwagwalada.

A wani labarin kuma, Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwa ye ba kawo yanzu mun samu labarin sun yi kwanton bauna inda suka kuma farma Manjo janar John Malu hari a kauyen sa na Tse Adoo dake a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue dake arewacin Najeriya.

Sai dai dai kamar yadda muka samu, cikin kankanin lokaci masu tsaron lafiyar sa suka mayar da martani ga 'yan bindigar suka kuma samu nasarar watsa su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel