Dan ƙunar bakin wake ya kashe kansa mutum guda, da raunata 4 a Borno

Dan ƙunar bakin wake ya kashe kansa mutum guda, da raunata 4 a Borno

- Wani 'dan kunar bakin wake ya tashi bam din jikinsa a Borno

- Wanda hakan ya janyo mutuwarsa da kuma wani mutum guda tare da raunata wasu

Wani ɗan ƙunar bakin wake ya raunata mamban ƙungiyar tabbatar da tsaro ta Civilian JTF huɗu tare kashe guda har lahira bayanda ya saki madannin bam ɗin dake maƙale a jikinsa.

Harin bam ya kashe mutum biyu tare da jikkata huɗu a Maiduguri

Harin bam ya kashe mutum biyu tare da jikkata huɗu a Maiduguri

Mataimakin kwamishinan ƴan sanda na jihar mai kula da aikace-aikace Mr Wakil Maye ne ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) faruwar lamarin a Maiduguri jiya Litinin.

Ya ce tashin bam ɗin ya faru ne a kan titin Baga da misalin karfe 1:00am na dare.

Maye bayyana cewa jami'an sintirin CJTF ne suka hango ɗan ta'addan daga nesa "Amma ko da ya ga zasu kama shi kafin ya isa inda yake hari, kawai sai ya tayar da bam ɗin, wanda hakan ta sanya ya kashe kansa da kuma wa ɗan CJTF guda gami da raunata ƙrin wasu huɗu".

KU KARANTA: Ba-kan-ta: 'Yan bindiga sun yi kwanton bauna sun kai wa babban janar din sojan Najeriya hari a Arewa

Tuni hara an aike da jami'an ganowa da kuma kwance abubuwa masu fashewa (EOD) domin tantance wurin da kuma ɗebe duk fasassun abubuwan wurin.

Mai magana da yawun jami'an sintin ta CJTF Malam Bello Danbatta ya tabbatar da cewa guda daga cikin mambobin ƙungiyar rasa ransa yayin ƙoƙarin ƙare ƙasarsa Najeriya daga harin ƴan ta'adda.

Dambatta ya kuma ƙara da cewa, ɗan ƙunar bakin waken yana burin zuwa inda ƴan uwa musulmai suke sallar dare (Tahajjud) a cikin goman ƙarshe na watan Azumi Ramadan domin dacewa da ganin Laylattul Qadri.

Ragowar huɗun da suka jikkata kuma an kai su asibitin jihar domin bmyi musu magani, shi wanda ya rasun an miƙawa iyalansa shi domin jana'iza.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel