Duk da kassara magoya bayan Buhari a majalisa, an gano suna kara yawa da karfi

Duk da kassara magoya bayan Buhari a majalisa, an gano suna kara yawa da karfi

- Magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari suna karuwa a majalisar dattawa da wakilai

- Wannan ya biyo bayan haramta ayyukan kungiyar da Bukola Saraki ya yi a kwanakin baya

- An kafa kungiyar ne bayan badakallar canja jadawalin zabe da ya yi sanadiyyar dakara da Sanata Ovie Omo-Agege

Binciken jaridar Daily Trust ya gano cewa Sanatoci da 'yan majalisar wakilai suna ta kara tururuwa wajen shiga kungiyar goyon bayan Buhari 'Buhari Parliamentary Group (PSG) duk da cewa Bukola Saraki ya tartwatsa kungiyar.

Sanatocin da yan majalisar wakilai da suka shiga kungiyar bayan zaman hadin gwiwa da akayi tsakanin Majalisar dattawa da Majalisar wakilai sun bayyana cewa sun shiga ne don ra'ayin kansu.

Duk da kassara magoya bayan Buhari a majalisa, an gano suna kara yawa da karfi

Duk da kassara magoya bayan Buhari a majalisa, an gano suna kara yawa da karfi

KU KARANTA: Kan 'yan majalisa ya rabu a kan dambaruwar dake faruwa tsakanin Buhari da Obasanjo

Wadanda suka fara kafa kungiyar ne a Majalisar Dattawa sun bayyana cewa sun kafa kungiyar ne don kare manufofin shugaba Muhammadu Buhari.

An kafa kungiyar ne bayan gabatar da kudirin neman canja jadawalin zaben 2019 da akayi a watan Fabrairun 2018 inda ake son fara gabatar da zaben yan majalisa, sannan na gwamnoni da yan majlisan jihohi sannan na shugaban kasa ya zo daga katrshe.

Sai dai Sanatoci kamar su Abdullahi Adamu da Ovie Omo-Agege da sauransu sun ki amincewa da dokar kuma daga baya su ka hada suka kafa kungiyar ta PSG.

Sanata Omo-Agege ya ce ana son yin canjin jadawalin zaben ne don musguwana shugaba Muhammadu Buhari. Hakan yasa akayi bincike akansa da wasu kuma daga baya aka dakatar dashi na kwanaki 90 sai dai kotu ta soke dakatarwar.

Majalisar dattawan har ila yau da haramta ayyukan kungiyar ta PSG inda ta ce baza ta amince da kafuwar kungiya irin wannan ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel