Kan 'yan majalisa ya rabu a kan dambaruwar dake faruwa tsakanin Buhari da Obasanjo

Kan 'yan majalisa ya rabu a kan dambaruwar dake faruwa tsakanin Buhari da Obasanjo

- Kawunnan yan majalisar wakilai na APC da PDP ya rabu game da batun sharri da Obasanjo ya yi ikirarin Buhari na yi masa

- A cikin kwanankin nan ne Obasanjo ya yi ikirarin cewa Shugaba Buhari yana shirya makircin kulle shi a kurkuku

- Yan APC sunyi ikirarin cewa Obasanjo bashi da gaskiya ne yayin da yan PDP su na goyon bayan Obasanjo

Kawunnan mambobin majalisar wakilai na jami'iyyar APC da PDP ya rabu game da zargin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi na cewa shugaba Muhammadu Buhari ya na shirya masa makirci don ya garkame shi a kurkuku.

Kan 'yan majalisa ya rabu a kan dambaruwar dake faruwa tsakanin Buhari da Obasanjo

Kan 'yan majalisa ya rabu a kan dambaruwar dake faruwa tsakanin Buhari da Obasanjo

Idan ba'a manta ba, Legit.ng ta kawo muku rahoton da Cif Olusegun Obasanjo ya koka game da makircin da Shugaba Buhari ke shirya masa ta hanyar amfani da takardun bogi da shedun karya don kulle shi a kurkuku.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 8 a arangamar da 'yan baranda su kayi da 'yan banga a Sakkwato

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yayin da 'yan majalisar APC ke goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari, takwarorinsu na jam'iyyar PDP sun ce akwai yiwuwar gaskiya cikin korafin na Obasanjo kuma ya kamata ayi bincike a kan batun.

Bulaliyar majalisa wanda dan jam'iyyar APC ne, Alhassan Ado-Doguwa ya ce: "Tabbas, marasa ko a ruwa suna zufa. Ya ce haure-hauren da Obasanjo ya keyi ba wani abu banne illa alamar rashin gaskiya. Bai dace 'yan Najeriya su manta da badakallar kudaden da suka faru karkashin gwamnatin Obasanjo ba.

"Zunzurutun kudi $16 biliyan da aka kashe wajen samar da wutan lantarki, da kuma almubarzanci da akayi wajen sayar da kayayakin gwamnati ga yan kasuwa da kuma wadaka da kudaden asusun kasar wajen na Najeriya na kadan daga cikin abubuwan da ya kamata a bincika.

"Ina fata irin wadannan hayaniyar na Obasanjo da zasu kawar da hankalin hukumomin yaki da cin hanci d rashawa ba."

Sai dai wani dan majalisar daga jihar Kogi (PDP), Karimi Sunday, ya yi ikirarin cewa Obasanjo yana da hurumin sannin wasu bayanai da ba kowa bane zai iya sani saboda haka ya dace a saurare shi saboda akwai yiwuwar gaskiya cikin lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel