Adams Oshimhole ya bayyana abinda zai faru idan bai samu zama shugaban jam’iyyar APC ba

Adams Oshimhole ya bayyana abinda zai faru idan bai samu zama shugaban jam’iyyar APC ba

Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewar, ko ya samu shugabancin jam’iyyar APC ko bai samu ba zai cigaba da yin aiki tukuru domin cigaban tad a tabbatar da ta cigaba da mulki a Najeriya.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne jiya, Litinin, a Abuja bayan kwamitin zaben shugabannin jam’iyyar na kasa ya tantance shi tare da bayyana cewar hanyar da ake bi domin zaben sabbin shugabannin ta fi muhimmanci a kan waye zai zama shugaban jam’iyyar.

Adams Oshimhole ya bayyana abinda zai faru idan bai samu zama shugaban jam’iyyar APC ba

Adams Oshimhole

Ni na yarda da dimokradiyya da siyasa ba da gaba ba, hakan ya saka na soki yunkurin karawa zababbun shugabannin jam’iyya wa’adi ba tare da gudanar da zabe ba. Duk da akwai matsaloli a cikin tsarin dimokradiyya, amma ta fi dacewa da jama’a a kan duk ragowar nau’in shugabanci,” a cewar Oshiomhole.

DUBA WANNAN: Akwai matsla: Gamayyar kungiyoyin kwadago sun bawa shugaba Buhari wa'adin kwana 21 ko su tsunduma yajin aiki

Sannan ya cigaba da cewa, “ina mai farin cikin cewar zan kara gwabzawa da mutumin da na sani domin mun taba yin takara tare kafin yanzu. Ya yi min magudi ya samu nasara saidai daga baya gaskiya tayi halinta na karbi shugabancin day a yi min fashin sa. Na kayar das hi zabe har a mazabar sa lokacin da sake tsayawa takarar neman gwamna a karo na biyu duk da sun tunzura mutane cewar nib a dan siyasa ba ne.”

Oshiomhole ya bayyana cewar ba ya shakkar zai samu nasarar lashe zaben shugabancin jam’iyyar da za a yi kwanan nan tare da jaddada cewar ko bai yi nasara ba zai cigaba da aiki tukuru domin cigaban jam’iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel