Akwai matsala: kungiyoyin kwadago sun bawa Buhari wa’adin kwanaki 21 ko su daka masa yaji mai zafi

Akwai matsala: kungiyoyin kwadago sun bawa Buhari wa’adin kwanaki 21 ko su daka masa yaji mai zafi

Kungiyoyin ma’aikatan Najeriya karkashin inuwar kungiyar “All Workers Convergence (AWC) tayi barazanar dakawa gwamnatin Najeriya yaji mai zafi matukar shugaba Muhammadu Buhari bai fito fili ya shaidawa ma’aikata cewar za a yi masu Karin albashi a watan Satumba ba cikin kwanaki 21.

Da suke ganawa da manema labarai a dakin taron dake sakatariyar AWC ta garin Ibadan, jihar Oyo, shugabannin kungiyar sun yi watsi da maganar da ministan kwadago, Dakta Chris Ngige, ya yi na cewar mai yiwuwa gwamnatin tarayya ba zata iya cika alkawarin da ta dauka na yiwa ma’aikata Karin albashi a watan Satumba ba.

Akwai matsala: kungiyoyin kwadago sun bawa Buhari wa’adin kwanaki 21 ko su daka masa yaji mai zafi

Shugaba Buhari

Sun yi barazanar cewar muddin gwamnati bata fito fili cikin kwanaki 21 ta jaddada cewar batun Karin albashin na nan daram ba, to tabbas zasu tsunduma kasa baki daya cikin yajin aiki.

Shugaban kungiyar AWC, Kwamred Andrew Emelieze, ya shaidawa ‘yan jarida cewar, “matukar gwamnati ta gaza cika alkawari, ya tabbata bata damu da bukatar ma’aikaci ba balle su inganta yanayin rayuwar sa, yin hakan tamkar nuna rashin tausayi ne ga halin da ma’aikata ke ciki.”

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya zayyanawa firaministan kasar Moroko halayen 'yan Najeriya

Sannan ya kara da cewa, “ina kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da fito ya tabbatar mana da cewar maganar Karin albashi na nan daram cikin kwanaki 21 masu zuwa ko kuma mu shiga yajin aiki. Zamu yi yajin aikin jan kunne na kwana daya, ranar 2 ga watan Yuli kafin daga bisani mu shiga na sai-baba-ta-gani matukar bamu samu tabbas daga wurin gwamnati ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel