Shugaba Buhari ya zayyanawa firaministan kasar Moroko halayen ‘yan Najeriya

Shugaba Buhari ya zayyanawa firaministan kasar Moroko halayen ‘yan Najeriya

A yau ne shugaba Buhari, kafin ya dawo gida Najeriya, ya shiadawa firaministan kasar Moroko cewar, babban abinda Najeriya ke Gadara da shi a matsayin ta na kasa shine kaifin basirar mutanen ta da kuma aikin su tukuru wajen neman na kan su.

A ganawar sa da Firaministan kasar ta Moroko, Saadeddine Othmani, a fadar sarkin kasar, shugaba Buhari ya ce dumbin yawan jama’ar dake Najeriya na aiki tukuru domin ganin kowa ya bayar da gudunmawar sa wajen kawowa kasar cigaba.

’Yan Najeriya mutane ne masu kaifin basira da matukar aiki tukuru. Na karbi bakuncin wasu dalibai ‘yan Najeriya dake karatu a nan Moroko kuma nayi matukar farinciki da irin kwazon su. Sun matukar burge ni,” a cewar shugaba Buhari.

Shugaba Buhari ya zayyanawa firaministan kasar Moroko halayen ‘yan Najeriya

Shugaba Buhari a kasar Moroko

Sannan ya cigaba da cewa, “muna da yawan matasa a Najeriya, kuma muna aiki domin ganin mun inganta rayuwar su ta hanyoyi daban-daban domin su bayar da gudunmawa wajen gina tattalin arziki mai karfi.”

DUBA WANNAN: An gano abinda yasa Obasanjo ya firgita da gwamnatin Buhari

Shugaba Buhari ya bayyana farincikin sa da yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla a kan shimfida bututun danyen man fetur da iskar gas daga Najeriya zuwa Morocco.

A jiya ne shugaba Buhari ya isa birnin Rabat na kasar Moroko a wata ziyarar ta wuni biyu day a kai kasar. A yau ne da yamma kuma ya dawo gida Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel