Masu haya 5 sun lalata yar mai gidansu mai shekaru 12 tare da yi mata ciki

Masu haya 5 sun lalata yar mai gidansu mai shekaru 12 tare da yi mata ciki

Wata babban kotun jihar Kano dake Igbosere ta saurari karan wasu maza biyar da aka zarga da lalata yarinyar maigidansu wanda ya mutu.

Dan sandan da ya shigar da karan, Sergeant Afeez Idowu, yayi zargin ne a gaban Justis Sedoten Ogunsanya lokacin da ake shari’an biyu daga cikin masu laifin, Shaibu Isiaka da John Obah.

Yan sanda ne suka gurfanar da Isiaka, 30, da Obah, 34, a gaban wata kotun majistare a 2014, akan chaji biyu da ya hada da lalata.

Masu haya 5 sun lalata yar mai gidansu mai shekaru 12 tare da yi mata ciki

Masu haya 5 sun lalata yar mai gidansu mai shekaru 12 tare da yi mata ciki

An tura shari’an babban kotu ne inda daga bisani gwamnatin jihar Lagas ta dauki shari’an.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun kwanaki 2 don bikin karamar sallah

Idowu, wanda ya jagoranci shari’an ya bayyana cewa yarinyar tare da mahaifiyarta sun bayyana Isiaka da Obah cikin mutane biyar din da suka lalata ta a lokuta daban-daban.

Yayi zargin cewa wadanda ake zargin sun amsa laifin su ba tare da bata lokaci ba a hedkwatan yan sanda dake Oworonshoki.

An bayyana cewa masu laifin kan ba yarinyar kudi ta siya kayan tande-tande sannan suce ta rike chanji idan suka aike ta.

Hakan ya basu daman yin lalata da ita a duk lokacin da mahaifiyarta ta fita har ya kai ga sun dura mata ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel