Kayode da Fayemi: Rigima ta kaure tsakaninsu kan kudaden da Ekiti ke tara wa a wata tun 2014

Kayode da Fayemi: Rigima ta kaure tsakaninsu kan kudaden da Ekiti ke tara wa a wata tun 2014

- Zaben Ekiti ya matso, hannun karba hannun mayarwa?

- A watan gobe ne za'a fara faafatawa tsakanin sabo da tsohon gwamna

- Dan takarar gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, a ranar litinin ya zargi Gwamnatin Gwamna Ayo Fayose da samar da tsananin rayuwa a shekaru hudu da suka shude

Kayode da Fayemi: Rigima ta kaure tsakaninsu kan kudaden da Ekiti ke tara wa a wata tun 2014

Kayode da Fayemi: Rigima ta kaure tsakaninsu kan kudaden da Ekiti ke tara wa a wata tun 2014

Fayemi da Fayose, wanda ya bayyana zargin a tataunawa da sukayi da manema labarai a Ado-Ekiti, yace Gwamnatin jihar ya kawo tsanani ga ma'aikata, dalibai, iyaye, yan kasuwa da masarautun gargajiya.

Yace bayan albashin ma'aikatan da ta rike na wata biyar zuwa tara, Gwamnatin jihar ta kasa biyan masarautun gargajiya alawus din da ake biyan su.

Dan takarar APC ya soki gwamnan na kasa bayyana yanda ake samar da kudin shiga na jihar tunda ya hau mulki.

"Kudin shiga na jiha ya kai Naira miliyan 600 duk wata kafin in bar ofishin saboda muna bayyana duk abinda ya shigo duk wata, amma babu wanda ya kara Jin kudin shiga na jihar Ekiti tunda na bar ofishin."

DUBA WANNAN: An yi gyara kan gadar Jebba da ta rufta

Kamar yanda yace, Gwamnatin bata da wani uzuri na rike wa ma'aikatan kudi tunda akwai shige da ficen kudade daga asusun kasar, kudin shiga da kuma kudaden da Gwamnatin tarayya ke badawa.

Dan takarar yayi alkawarin canza jihar in dai aka zabe shi.

Fayemi yayi alkawarin zai tabbatar da qudurorin shi takwas don tabbatar da jihar Ekiti na samun cigaban da ya kamata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel