Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun kwanaki 2 don bikin karamar sallah

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun kwanaki 2 don bikin karamar sallah

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Juma’a, 15 ga watan Yuni da Litinin, 18 ga watan Yuni amatsayin ranar hutu domin barin Musulman Najeriya sun yi bikin karamar sallah na 2018.

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ne ya sanar da hakan.

Dambazau yayi sanarwan ne a ranar Litinin, 11 ga watan Yuni a Abuja a madadin gwamnatin tarayya a wata sanarwa daga M Umar, sakataren din-din-din na ma’aikatar cikin gida.

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun kwanaki 2 don bikin karamar sallah

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun kwanaki 2 don bikin karamar sallah

NAN ta ruwaito cewa ministan ya taya yan uwa masulmai murnar kammala azumin Ramadana cikin nasara sannan kuma ya bukaci dukannin musulman Najeriya da suyi amfani da bikin wajen yiwa kasa addu’an samun zaman lafiya, hadin kai, cigaba da kuma daidaituwa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya isa Abuja bayan ziyarar da ya kai kasar Maroko

Ya kuma bukaci dukkanin al’umman Najeriya da su taimakawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen kawo cigaban kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel