Wani matashi ya hau kololuwar karfen sabis zigidir domin gudun kamun ‘yan sanda

Wani matashi ya hau kololuwar karfen sabis zigidir domin gudun kamun ‘yan sanda

Wani matashi, Anthony Murimi, ya jawo barkewar hargowa bayan yah aye kan kololuwar karfen sabis tsirara tare da tube kayan sa domin gujewa kamun ‘yan sanda.

A yau, Litinin, ne hukumar ‘yan sanda ta gurfanar da matashin mai shekaru 23 a gaban wata kotu dake Embu a kasar Kenya bisa tuhumar sa da yunkurin kasha kan sad a kuma yin kutse cikin muhallin dab a shi da hurumin shiga.

Wani matashi ya hau kololuwar karfen sabis zigidir domin gudun kamun ‘yan sanda

Matashi ya hau kololuwar karfen sabis

Murimi ya amsa dukkan laifukan sa tare da neman kotun tayi masa afuwa bisa abinda ya aikata.

Ana tuhumar matashin, Murimi, tare da wani wanda ya taimaka masa da aikata laifi tsallaka wayar dake kewaye da karfen sabis mallakar kamfanin Safaricom, lamarin da ya tayar da hankalin jama’ar yankin da kuma masu kula da karfen.

DUBA WANNAN: Tsohon babban dan sanda ya bayyana dalilin firgitar Obasanjo da gwamnatin shugaba Buhari

Matashin ya sauko daga kan karfen ne bayan ‘yan sanda sun kama abokin sa da ya taimaka masa wajen hayewa kan karfen.

Kotu ta bukaci a gabatar mata da rubutaccen rahoton laifukan matashin cikin kwana bakwai (7) tare da daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Yuni, 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel