Sai a nemi Jannareto: Ku shiryawa fuskantar rashin samun wuta a lokacin Damuna – Fashola

Sai a nemi Jannareto: Ku shiryawa fuskantar rashin samun wuta a lokacin Damuna – Fashola

- Rashin wutar lantarki zai kara kamari musamman a yanayin damunar nan

- Ministan samar da wutar lantarki Babatunde Fashola ne ya shaida hakan

- A don haka ne yayi kira ga kamfanin rarraba wutar lantarkin da su tanadi kayan gyara a hannu

Ministan aiyuka, makamashi da gidaje Babatunde Fashola ya shaidawa ‘yan Najeriya yau Litinin cewa su shiryawa fuskantar katsewar wutar lantarki sakamakon cigaba da samun saukar ruwan sama a yanayin damunar da ake ciki

Sai a nemi Jannareto: Ku shiryawa rashin samun wuta a lokacin damuna – Minista ya fadawa ‘yan Najeriya
Sai a nemi Jannareto: Ku shiryawa rashin samun wuta a lokacin damuna – Minista ya fadawa ‘yan Najeriya

Ya ce daga cikin irin kalubalan da ma’aikatar wutar lantarkin ke fuskanta sun hada da; yawaitar samun tsawa da walkiya da kuma iska mai karfin gaske da take janyo yawaitar faduwar bishiyoyi da turakun dakon wayar lantarki da sauransu.

Sai a nemi Jannareto: Ku shiryawa rashin samun wuta a lokacin damuna – Minista ya fadawa ‘yan Najeriya
Sai a nemi Jannareto: Ku shiryawa rashin samun wuta a lokacin damuna – Minista ya fadawa ‘yan Najeriya

Daga nan ne Ministan ya tabbatar da cewa yana da yakinin kamfanunuwa rarraba wutar lantarkin zasu zage damtse domin fuskantar wannan kalubale dake tafe ta hanyar samar da kayan gyaran da ya kamata domin magance matsalar.

KU KARANTA: Muje zuwa: Fashola yayi alƙawarin gyara Gadar Mowo da ta rufta nan da awa 72h

“A watanni baya mun tattauna da kamfanin dake rarraba wutar lantarki kan yadda za’a kara kaimi domin cigaba da gyara kaya yayin da suka samu matsala”.

“Yanzu kuma yayin zamanmu ina so mu mayar da hankalinmu wajen fuskantar damunar bana da kuma sha’anin da take tafe da shi saboda tsawa da kuma iska mai karfi”. Fashola ya jaddada yayin zamansa da masu ruwa da tsaki a harkar samar da wutar lantarki. Ministan ya bayyana hakan yayin wani zama da masu hannu da tsaki a samar da wutar lantarki

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel