Wani babban tsohon dan sanda ya bayyana dalilin da yasa Buhari ke firgita Obasanjo

Wani babban tsohon dan sanda ya bayyana dalilin da yasa Buhari ke firgita Obasanjo

- Tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Legas, Abubakar Tsav, ya ce shekaru 8 da Obasanjo ya yi a mulki cike suke da magudi da yiwa doka karan tsaye

- Ya jinjinawa shugaba Buhari bisa umarnin day a bawa shugaban rundunar ‘yan sanda na sake bude kundin binciken kisan tsohon ministan shari’a, Bola Ige

- Gwamna Ayode Fayose ya shawarci Obasanjo ya mika kan sa a bincike shi idan yana da gaskiya ko hujjojin kare kan sa

Tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Legas, Abubakar Tsav, ya bayyana cewar ba wani abu ya firgita tsohon shugaban kasa Obasanjo ba sai irin ta’adin da ya tafka a cikin shekaru 8 da ya yi yana mulki.

Tsav ya bayyana cewar, kwarmaton da Obasanjo ke yin a cewar Buhari zai kama shi ya kulle, ya tabbatar da cewar yana tsoron irin zunuban da ya aikata a ofis, lokacin da yake mulki.

Wani babban tsohon dan sanda ya bayyana dalilin da yasa Buhari ke firgita Obasanjo

Abubakar Tsav

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito Tsav na fadin cewar, shekaru 8 da Obasanjo ya yi a mulki cike suke da badakala kala-kala.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: 'Yan sanda sun kara bankado wata dangantaka mai karfi tsakanin Saraki da 'yan fashin Offa

Da yake bayar da misalan irin badakalar da Obasanjo ke tsoron a binciko sun hada da batun kisan wasu manyan ‘yan siyasa da suka hada da tsohon ministan shari’a, Bola Ige, da kuma badakalar cin hanci da suka hada da kasha biliyan $16bn na wutar lantarki.

Tsav ya kara da cewar, Obasanjo mai laifi ne kuma dole ya firgita duk lokacin da ya ji za a binciki gwamnatin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel