Za mu mayar da gidan karuwai da aka rusa makarantu – Gwamna Kashim Shettima

Za mu mayar da gidan karuwai da aka rusa makarantu – Gwamna Kashim Shettima

Gwamnatin jihar Borno a ranan Juma’a ta bayyana cewa za ta mayar da gidan karuwai da ke Galadima a Maiduguri makarantun gwamnati domin amfanin al’umma.

Gwamna Shettima wanda ya kai ziyara unguwar domin duba yadda aka rusa gidan karuwan ya bayyana cewa hakan ya zama wajibi domin kawar da yan ta’adda da bata gari a Jihar.

Gwamnatin ta nada kwamiti na musamman karkashin jagorancin kwamishanan shari’a na jihar, Justice Alhaji Kaka Shehu Lawan, domin rusa dukkan wani ginin bata gari a unguwar domin cigaba da yakin rashin tarbiyya a garin.

“Babu makaranta a unguwarnan. Muna da daman gina makarantu domin kawo cigaban jam’a,”

Za mu mayar da gidan karuwai da aka rusa makarantu – Gwamna Kashim Shettima

Za mu mayar da gidan karuwai da aka rusa makarantu – Gwamna Kashim Shettima

Gwamna Shettima ya jinjinawa mambobin kwamitin da wannan kyakkyawan aiki da suka yi.

KU KARANTA: Yadda wasu mutane 4 suka hallaka abokinsu suka guntule zuciyarsa

A cewarsa: “Kun yi aiki mai kyau, na jinjina muku, duk inda kuka ga bata gari na baku daman daukan mataki ba tara bata lokaci ba. Ku yi aiki bisa ga dokar kasa.”

“Wajibi ne mu yaki barandani da dani’u maras amfani. A nan ake sayar da muggan kwayoyi, mabuyar yan baranda, barayi da ya ta’adda ne.”

Za mu mayar da gidan karuwai da aka rusa makarantu – Gwamna Kashim Shettima

Za mu mayar da gidan karuwai da aka rusa makarantu – Gwamna Kashim Shettima

Idan baku manta ba, Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa gwamnatin jihar Borno ta fitittiki yan gidan magajiya da gidajen giya a babban birnin jihar Maiduguri.

Za mu mayar da gidan karuwai da aka rusa makarantu – Gwamna Kashim Shettima

Za mu mayar da gidan karuwai da aka rusa makarantu – Gwamna Kashim Shettima

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel