Badakalar N500m: Jami’an gwamnatin Yuguda a Bauchi sun shiga tsaka mai wuya

Badakalar N500m: Jami’an gwamnatin Yuguda a Bauchi sun shiga tsaka mai wuya

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta gurfanar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi Babayo Gamawa tare da wasu mutane biyar a babbar kotun jihar.

An gurfanar da su ne akan zargin lamushe kudi har Naira miliyan 500 da suka yi a lokacin da suke rike da kambun gwamnatin jihar.

Cikin wadanda hukumar EFCC ta guranar sun hada tsohon sakataren gwamnatin jihar Bauchi Ahmed Dandija da Aminu Hamayo, tsohon kwamishinan filaye Dahiru Madaki, babban mashawarcin tsohon gwamna Isa Yuguda kan al’amuran aikin Hajji Sanusi Sarkin -Aska, tsohon mamba a majalisar dokokin jihar Bauchi Aliyu Jallam.

Lauyan hukumar EFCC ya roki kotu da ware sunan Dandija daga cikin jerin sauran domin a fara yi musu shari’a.

Sai dai lauyan dake kare Dandija, Nasiru Malam ya ki amincewa da hakan cewa hukumar EFCC ta gurfanar da mutanen shida kan laifi daya amma ba biyar.

Badakalar N500m: Jami’an gwamnatin Yuguda a Bauchi sun shiga tsaka mai wuya

Badakalar N500m: Jami’an gwamnatin Yuguda a Bauchi sun shiga tsaka mai wuya

Malam ya ce Ahmed ya kasa zuwa kotun ne a wannan rana sakamakon rashin lafiya da yake fama da ita.

Ya ce saboda wannan dalili yana rokon kotun da ta dakatar da shari’ar har sai Dandija ya dawo kafin ta fara gudanar da shari’a.

KU KARANTA KUMA: 2019: Talakawa ne zasu yanke hukunci kan wanda zai zamo shugaban kasar Najeriya na gaba - Keyamo

Sannan ya koka cewa Dandija bai samu takardar gayyatar ya bayyana a kotu ba har yanzu.

A karshe, alkalin kotun Muhammed Shitu ya amince da rokon lauyan sannan ya umurci rajistaran kotun da ya gaggauta aikawa Dandija da takardar gayyata kafin kotun ta sake zama.

Za a ci gaba shari’ar a ranar 25 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel