Da yiwuwar kacamewar hatsaniya tsakanin mahauta da makiyaya a jihar Oyo

Da yiwuwar kacamewar hatsaniya tsakanin mahauta da makiyaya a jihar Oyo

- Wani malamin addini ya bayyana fargabarsa da tashin hankalin da ka iya faruwa a dalilin hada mahauta da makiyaya wuri daya

- Ya ce garin neman samun ribar kafa mayankar dabbobi ake shirin kai su a baro

- A bisa haka ne ya bayyana rashin amincewarsu da wannan sabon tsari da kuma kira da a canza musu wuri

Wani malami yayi hasashen tasowar hadarin rikici a dalilin canzawa mayankar dabbobin zuwa kusa da makiyaya a kauyen Amosun dake karamar hukumar Akinyele na jihar ta Oyo.

Da yake magana ta bakin wani mai fafutukar kare hakkin bil Adama Pasto Tunji Hamzat Jigan, ya ce kusancin mayankar dabbobin da wanzuwar makiyayan tamkar wata kunamar bindiga ce da ka iya tashi a kowanne loakci.

Da yiwuwar kacamewar hatsaniya tsakanin mahauta da makiyaya a jihar Oyo

Da yiwuwar kacamewar hatsaniya tsakanin mahauta da makiyaya a jihar Oyo

“Kusancin makiyayan da mahauta a kauyen Amasun ka iya janyo tashin hankali mai girman gaske. Don haka dawo da su da akayi wannan kauye kan iya zamowa sanadiyyar fitina babba a jihar baki daya”.

KU KARANTA: An kori jami’an ‘yan sanda 8 daga aiki a jihar Legas, karanta laifukan da suka aikata

Pastor Jigan ya dai ala wadai da wannan sauyin wuri da aka yi, inda aka jiyo shi yana cewa kawai don wasu na kokarin cin riba ba abu ne da ya dace a jefa rayuwar mazauna yankin a cikin hadari ba.

Amma sai dai shugaban kungiyar cigaban yankin na Aare Latosa Bashorun Adekunle Oladeji, ya ce akwai yiwuwar su bada wa’adin kwanaki uku domin mahautan su koma can ainihin babbar mahautar garin.

Sannan ya cigaba da cewa “Mun sa cewa umarnin da gwamnati ta bayar ta yi shi ne don cigaban mutanen jihar musamman mahautan, a don haka ne ma yayi kira ga uwar kungiyar mahautan da ta gaggauta umartar ‘ya’yanta da su koma sabuwar mayankar da aka aka gina domin tsaftace harkar yankawa da gyran naman”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel